Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)

Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)

- Bayan matasan Calabar sun saci kayan tallafi da dukiyoyin gwamnati da na al'umma, Gwamnan jihar ya lashi takobin hukunta su

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh ya tura jami'ansa binciken gidaje don kwaso kayan, tare da kama wadanda aka gani dasu

- Matasa sun fara ajiye kayan a bakin tituna, bololi da wuraren buya, cikin kayan har da katifun asibiti, talabijin, janareto, kayan abinci da sauransu

Bayan Jami'an tsaro sun fara bincike gidaje don nemo dukiyoyin gwamnati da na mutane wadanda aka sata, bata-gari sun fara yasar da kayan a bololi da kuma wasu wuraren buya a cikin garin.

Wannan lamarin ya faru ne bayan kwamishinan 'yan sanda, Abdulkadir Jimoh ya umarci duk wanda ya saci kayan da ya dawo da su cikin awanni 24, ko kuma ya fuskanci fushin hukuma.

Idan ba'a manta ba, cikin kwanakin karshen mako ne bata-gari da ke babban birnin Calabar suka balle ma'adanar jihar da sunan zanga-zangar EndSARS, suka sace duk wasu kayan tagomashin tallafin COVID-19, dukiyoyin gwamnati da na al'umma ba'a barsu a baya ba.

Sakamakon haka ne aka sa kulle mai tsanani a manyan tituna da ke Calabar ta kudu wadanda zasu shiga kananan hukumomi da ke tsakiyan jihar, Vanguard ta wallafa.

Matasan Mbukpa, Edibedibe, Calabar ta kudu, Eta Agbor, Ikot Effa, Asari da birnin jihar Calabar sun fara ajiye kayan da suka sata a bakin tituna da bololi.

A kasuwar Mbukpa kuwa an ajiye wasu daga cikin kayan da aka sato daga asibitoci wadanda ake zargin suna da cututtuka tattare da su. A Edibedibe kuwa an ajiye kayayyakin amfani na wutar lantarki a bakin tituna, ciki har da kayan kallo, katifu, janareto da gadaje.

Dama gwamna ya lashi takobin matsawar ya gano wadanda suka yi wannan aika-aika to sai sun fuskanci fushin hukuma don ba zai kyalesu su lalata garinsu na gado ba.

Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo)
Bayan binciken gida-gida, jama'a sun fara mayar da kayayyakin da suka sata (Bidiyo). Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tallafin korona: Wasu jihohi sun fito da kayan abinci, sun fara raba wa talakawa

KU KARANTA: Da duminsa: Gagarumar gobara ta lashe kayan gini a kasuwar Dei Dei a Abuja

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel