Duk da gida bai koshi ba: Nigeria za ta kai wa Chadi wutar lantarki

Duk da gida bai koshi ba: Nigeria za ta kai wa Chadi wutar lantarki

- Gwamnatin Nigeria ta shirya tsaf domin fara aikawa Chadi wutar lantarki, duk da cewa da ma can tana aikawa jamhuriyar Niger, Benin da Togo

- A halin yanzu, cibiyoyi 27 bakwai ne ke rarraba wutar lantarki a Nigeria, yayin da 11 ba sa aiki, kuma karfin wutar ya sauko zuwa 3,474.5MW

- Sai dai duk da wadannan matsaloli da kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa TCN ke fuskanta, ya ce Nigeria na da karfin aikawa Chadi wutar

Gwamnatin tarayya na duba yiyuwar kai wa jamhuriyar Chadi wutar lantarki, biyo bayan bukatar hakan da makwabciyar kasar ta gabatar.

Kamfanin rarraba wutar lantarki mallakin gwamnati ya bayyana hakan a ranar Lahadi a taron da aka gudanar makon da ya gabata don duba yiyuwar kai wa Chadi wutar lantarki.

A halin yanzu Nigeria na da karfin wuta tsakanin 3,000MW zuwa 4,500MW, kuma ko a yanzu, Nigeria na kai wutar lantarki ga jamhuriyyar Niger, Benin da Togo.

KARANTA WANNAN: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10

Wata sabuwa: Nigeria za ta kai wa Chadi wutar lantarki
Wata sabuwa: Nigeria za ta kai wa Chadi wutar lantarki - @MobilePunch
Asali: Twitter

A ranar Lahadi, karfin lantarkin ya sauko daga 3,474.5MW daga 3,776.5MW da ya ke a ranar Asabar, a cewar rahoton sashen kula da lantarkin Nigeria NESO.

Adadin cibiyoyin wutar kasar da ba sa samar da wutar lantarki sun haura zuwa 11 da misalin karfe 6 na safiyar Lahadi, daga 8 da ake da su a ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

Cibiyoyin da suka daina aiki, su ne; Geregu II, Sapele II, Alaoji, Olorunsogo II, Omotosho II, Ihovbor, Gbarain, Ibom Power, AES, ASCO da Trans-Amadi.

A halin yanzu, cibiyoyi 27 bakwai ne ke rarraba wutar lantarki a kasar, kuma suna karkashin kulawar kamfanin TCN.

A ranar 22 ga watan Yunin 2020 ne kamfanin TCN ya sanar da cewa gwamnatin Chadi ta bukaci gwamnatin Nigeria da ta dunga kai mata wutar Lantarki don saukaka matsalar lantar da suke yi.

Ya bayyana cewa jakan Chadi a Nigeria, Mr Abakar Chachaimi, ya gabatar da bukatar a lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa ga ministan makamashi, Mr Sale Mamman, a Abuja.

A wani labarin, Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) ta bada sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa kayayayyakin da aka kwashe daga ma'adanarta a yankin Narayi sun hada da magunguna masu tarin hatsari.

"Hukumar kamfanin abincin da aka kwashe musu kaya a ma'adanarsu da ke Kakuri sun tabbatar da cewa sun zuba wa masarar magunguna wanda hakan yasa ba zai yuw a ci ba,"

"Gwamnatin jihar Kaduna tana kira ga jama'a da su bayyana wadanda suka kwashe abincin da kuma inda suka boyesu domin gujewa hatsari," kwamishinan yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel