Rashin imani: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10

Rashin imani: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10

- Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu miji da mata, sakamakon kama su da laifin azabtar da karamar yarinya mai shekaru 8 da haihuwa

- Bincike ya nuna cewa, iyalan na azabtar da yarinyar ne, saboda ta shanye alawar N10 da suka sayo wa 'yarsu mai shekaru 2 da haihuwa

- Bidiyon yadda matar gidan ke dukan yarinyar bayan shanya ta a tsakiyar rana da kuma daure kafafunta, ya karade kafofin sada zumunta

A ranar Litinin ne rundunar 'yan sanda ta cafke wasu miji da mata, Mr da Mrs Philip Iboko, bisa zarginsu da azabtar da wata yarinya mai shekaru takwas da haihuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano iyalan suna azabtar da yarinyar ne biyo bayan bullar wani bidiyo a yanar gizo da ke nuna yadda aka shanya yarinyar a rana bayan da aka daure kafafunta.

Yarinyar da miji da matar na zama a gida daya tsawon shekaru biyu, kuma anga matar a cikin bidiyon tana azabtar da yarinyar.

KARANTA WANNAN: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

Rashin imani: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10
Rashin imani: Yadda miji da mata suka azabtar da karamar yarinya saboda alawar N10 - www.pinterest.com
Asali: UGC

Iyalan da ke zama a karamar hukumar Izzi da ke jihar Ebonyi, sun huce haushin su kan karamar yarinyar bayan da ta shanye alawar N10 da suka sayowa yarsu mai shekaru biyu.

Wata majiya ta tabbatar da cewa sai da makwaftan iyalan (Mr Chinedu da Mr Raymond) suka bayar da hakuri kana aka kwance yarinyar.

KARANTA WANNAN: Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

Makwaftan guda biyu, a cewar majiyar, sun kwance yarinyar suka cire ta daga cikin rana, kasancewar har ta galabaita sakamakon dukan da matar ta yi mata da kuma zafin rana.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi kan lamarin ya ci tura, kasancewar jami'ar hulda da jama'a ta rundunar ba ta amsa wayar ta.

A wani labarin, Mayakan ta'addancin Boko Haram masu tarin yawa sun sheka lahira a Ngwuri Gana da ke Junacheri a jihar Borno bayan ragargazar da aka yi musu ta jiragen yaki a maboyarsu.

A wata takarda sa shugaban fannin yadaabarai na rundunar soji, Manjo Jabar John Enenche ya fitar, ya ce hakan na daga cikin kakkabar da suke yi wa 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel