Da duminsa: Sojoji da 'yan daba sun yi musayar wuta a fadar basarake, mutum 7 sun rasu

Da duminsa: Sojoji da 'yan daba sun yi musayar wuta a fadar basarake, mutum 7 sun rasu

- Tashin hankali ya barke a karamar hukumar Irewole da ke jihar Osun, tsakanin 'yan ta'adda da sojoji a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba

- Kamar yadda wakilin Legit.ng na jihar Osun, Ibrahim Akinola, ya ruwaito, mutane fiye da 7 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin

- Rahotonni sun nuna cewa wani Yarima ne ya dauki nauyin 'yan ta'addan don su tayar da hankula, su kashe sarkin ya maye gurbinsa

Tashin hankali ya barke a karamar hukumar Irewole da ke jihar Osun, a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, bayan wasu 'yan ta'adda sun yi bata-kashi da sojoji.

Wakilin jaridar Legit.ng na jihar Osun, Ibrahim Akinola, ya ruwaito yadda sama da mutane 7 suka rasa rayukansu sakamakon dauki ba dadin.

Kamar yadda suka tattaro bayanai, 'yan ta'adda da suka nemi kai hari fadar Sarkin Akire, Oba Olatunde Folabi, inda sojoji suka yi yunkurin dakatar da su daga shiga fadar.

'Yan ta'addan sun fara jifan sojojin da duwatsu wanda hakan ne musabbabin tashin hankalin.

Kamar yadda rahoton yazo, 'yan ta'addan sun kwace bindigogi 4 daga hannayen sojoji har suna ji musu rauni, suka shige fadar sarkin.

An dauki sojojin da suka ji ciwon zuwa asibiti mafi kusa, daga nan wasu suka umarci bata-garin su mayar da bindigogin cikin mintuna 30.

Rashin mayar da bindigogin da 'yan ta'addan suka yi ne ya janyo kiran wasu sojojin, wanda hakan ya janyo harbe-harbe tsakaninsu, har aka rasa rayuka fiye da 7.

Kamar yadda daga baya aka gano, wani yarima ne ya turosu da sunan zanga-zangar EndSARS don su tayar da hankali ya amshe kujerar sarkin. Hakan ya janyo kashe-kashen mazauna wurin, ciki har da wasu daga cikin dangin yariman.

Kamar yadda wani wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce 'yan ta'addan sun daki sarakuna da dama da direbobinsu, sannan sun kwashe duk wani kayan tagomashi da ke cikin fadar, duk da kokarin da jami'an tsaro suka yi ta yi, amma hakan ya cimma tura.

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

Da duminsa: Sojoji da 'yan daba ana musayar wuta a fadar basarake
Da duminsa: Sojoji da 'yan daba ana musayar wuta a fadar basarake. Hoto daga Ibrahim Akinola
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami'ai uku a kan kone ofisoshin 'yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar.

A wata takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin, Kenneth Ugbala, a ranar Lahadi, ya ce mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai, Nchekwube Aniakor da wasu shugabanni uku, ya sallamesu.

Shugabannin da aka sallama sun hada da Amos Ogbonnaya, Jerry Okorie Ude da Martha Nwankwo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel