An kashe jami'in kwastam a jihar Jigawa, an gudu da bindigarsa
- Batagari sun kaiwa jami'an rundunar hukumar kwastam a kauyen Kyarma da ke yankin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa
- An kashe jami'in hukumar kwastam daya, an raunata daya tare da yin awon gaba da bindigoginsu
- Babu rahoton cewa an gudanar da zanga-zanga a jihar Jigawa
An kashe jami'in hukumar hana fasa kwauri (kwastam) tare raunata wan yayin wani hari da wasu batagari suka kai karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa, kamar yadda jaridar Thecable ta rawaito.
Abdul Jinjiri, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, ya ce batagrin sun kaiwa jami'an kwastam harin ne ranar Lahadi yayin da suka kai wani samame domin gudanar da bincike kamar yadda suka saba.
A cewar Jinjiri, batagarin sun yi awon gaba da bindigar jami'in kwastam din da suka kashe.
DUBA WANNAN: FG ta ci tarar manyan gidajen talabijin uku saboda kunyata gwamnati
"Jami'an rundunar 'yan sanda da ke karamar hukumar Ringim sun samu kiran ko ta kwana a kan cewa wasu batagari sun kaiwa jami'an kwastam hari yayin da suka je wani aiki a kauyen Kyarma ranar 25 ga watan Oktoba.

Asali: Depositphotos
"Batagarin sun kashe jami'in kwastam daya tare da raunata wanu guda, sannan ana zargin cewa sun yi awon gaba da bindigogi biyu mallakar jami'an," a cewar Jinjiri.
DUBA WANNAN: Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m
Jinjiri ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta fara kokarin ganin ta kama batagarin ta hanyar fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Zanga-zanagar luma ta neman a rushe SARS ta rikide zuwa kazamin rikici a jihohi da dama.
Sai dai, babu rahoton cewa mutanen jihar Jigawa sun gudanar da zanga-zangar ENDSARS.
Rundunar 'yan sanda ba ta bayyana wanne irin bincike jami'an kwastam suka je yi ba yayin da aka kai musu hari kauyen Kyarma.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng