Matar aure ta tsinke mazakutar mijinta bayan ya dirkawa wata budurwa ciki

Matar aure ta tsinke mazakutar mijinta bayan ya dirkawa wata budurwa ciki

- Matar aure a yankin Appawa da ke karamar hukumar Lau ta jihar taraba ta tsinke mazakutar mijinta

- Kamar yadda makwabtansa suka tabbatar, da sanyin asubahi suka shiga cetonsa bayan ihunsa da ya tashesu

- Matar ta tabbatar da cewa ta yi hakan ne saboda dirkawa wata budurwa ciki da yayi bayan ita ko haihuwa bata yi ba

Wata mata mai matsakaicin shekaru ta tsinke mazakutar mijinta a kan zarginsa da dirkawa wata budurwa ciki a yankin Appawa, wani bangare na karamar hukumar Lau na jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, mijin mai suna Babangida wanda aka fi sani da Bangis yana cikin shekarunsa na 30.

Ya samu miyagun raunika a mazakutarsa bayan da matarsa ta yi yunkurin tsinka masa mazakutar a ranar Lahadi.

Wata majiya daga yankin wacce ta sanar da The Nation, ta ce Bangis ya je kasuwa, bayan wahalar da ya sha sai ya isa gida inda ya kwanta bacci.

"Da asubahi, matarsa ta tsinke masa mazakuta saboda dirkawa wata mata ciki da yayi. Ya mayar da martani inda ya raunata ta da wukar da ya karbe a hannunta.

“Makwabta sun ji ihunsu inda suka garzaya cikin gidan tare da tarar da wannan lamarin," majiyar tace.

A lokacin da aka bukaci sanin dalilinta na kokarin tsinke masa mazakuta, matar ta yi martanin cewa ko a littafin bibul an bukaci a tsinke duk abinda zai sa a yi zunibi.

An mika Bangis asibiti kuma na gano cewa har a halin yanzu basu da da ko daya da matar.

KU KARANTA: Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10

Matar aure ta tsinke mazakutar mijinta bayan ya dirkawa wata budurwa ciki
Matar aure ta tsinke mazakutar mijinta bayan ya dirkawa wata budurwa ciki. Hoto daga @TheNation
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC

A wani labari na daban, Fusatattun matasa a karamar hukumar Yola ta jihar Adamawa sun garzaya ma'adanar tallafin rage radadin korona na jihar.

Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga matasan suna kokari har ta kai ga sun balle kofar ma'adanar inda suka dinga murna tare da ihu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel