Yawan arzikin Obama da kuma hanyoyin da ya bi wurin mallakarsu

Yawan arzikin Obama da kuma hanyoyin da ya bi wurin mallakarsu

- Tun bayan saukar Barack Obama daga mulkin Amurika, ya zage damtsensa wurin neman na tuwo

- Wasu daga cikin ayyukansa sun hada da rubuce-rubuce da kuma jawabi ga jama'a

- Yanzu haka ya tara dukiya mai kimanin yawan dala miliyan 40, daidai da naira biliyan 15.24

Tsohon shugaban kasar Amurika, Barack Obama, ya yi ta fafutukar neman nakansa tun bayan saukarsa karagar mulkin Amurka.

Wasu daga cikin ayyukansa sun hada da rubuce rubuce da kuma jawabi ga jama'a, Legit.ng ta ruwaito.

Business insider sun ruwaito cewa, an kiyasta dukiyar Obama ta kai dala miliyan 40, wanda hakan ya kai kimar naira biliyan 15.24

A tsawon shekaru 8 da yayi a matsayin shugaban kasa, ya tara dala miliyan 20, daidai da naira biliyan 7.62 da albashinsa a matsayinsa na shugaban kasa, hannayen jari da litattfan da ya rubuta.

Littafin da ya fara rubutawa shine 'Dreams from my Father' wanda ya saki a 1995, ya kara wallafawa a 2004.

Kamar yadda ya taba fadi lokacin kamfen: "Kafin littafina ya shahara, ni da iyalina na zaune ne cikin rufin asiri, kuma ina da motoci 2, wanda daya daga cikin ba wata motar a zo a gani bace."

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu

Yawan arzikin Obama da kuma hanyoyin da ya bi wurin mallakarsu
Yawan arzikin Obama da kuma hanyoyin da ya bi wurin mallakarsu. Hoto daga Getty Images/Mark Wilson/Scott Olson
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Yadda 'yan daba suka sace takardun makaranta na, fasfoti da kayan abinci - Dan majalisa

A wani labari na daban, cikin gaggawa gwamnonin jihohi 36 da ke Najeriya da babban birnin tarayya Abuja sun fara rarraba kayan abincin tallafin COVID-19, ba tare da jiran umarnin gwamnatin tarayya ba.

Tun ranar Larabar da ta gabata ne bata-gari suka fara balle ma'adanar kayayyakin tallafin COVID-19 na jihohi suna kwashe kayayyakin abinci da sunan zanga-zangar EndSARS.

A cikin kwanakin da suka gabata ne jihohi suka yi ta bayar da dalilan da suka hana su raba kayan tallafin tuntuni, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel