Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu

Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu

- Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata zargin adana kayan tallafin COVID-19 ba tare da rabawa talakawa ba

- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce mafi yawan gwamnonin sun adana ne idan guguwar COVID-19 ta biyu ta tashi, su rabawa talakawa

- Hakika suna iya kokarin ganin sun tabbatar da adalci ga duk dan Najeriya, kuma zasu kiyaye yin abubuwan da za'ayi musu mummunar fassara

Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19.

Kungiyar manyan 'yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyoyin nairori don taimakon 'yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992.

A cikin kudaden da suka hada an yi amfani da wasu don gina cibiyoyin kula da lafiya da magunguna cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da aka yi amfani da wani bangare na kudin don siyan kayan abinci don rabawa talakawan da ke fama da yunwa yayin zaman gida.

Bayan an bayar da kayan abincin ne gwamnatin jihohi suka killace su a ma'adanar su, suna tunanin yadda za su raba kayan abincin.

Bayan zanga-zangar EndSARS ne wasu bata-gari suka nemo adireshin ma'adanar da ke jihohi, suka shiga suka kwashe su tas, a jihohi kamar Legas, Osun, Taraba, Kaduna da sauransu.

Kamar yadda aka sani, Legas babban birni ne inda ake ajiye-ajiyen kayan amfani, ba kayan tallafin COVID-19 kadai ba.

Yanzu haka a cewar wasu jihohin, sun adana kayan tallafin ne idan guguwar COVID-19 ta biyu ta tashi, sai a rabawa talakawa.

Kungiyar gwamnonin Najeriya tace ya kamata gwamnoni su gyara yadda suke tafiyar da mulkinsu don kawo gyara, suyi iyakar kokarin su don ganin ba su yi abubuwan da za'ayi musu mummunar fassara ba.

NGF na iyakar kokarin ganin ta tabbatar da adalci da mulki mai inganci a Najeriya.

KU KARANTA: Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun fatattaki 'yan ta'addan da suka kai hari Borno

Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu
Gwamnonin Najeriya sun yi martani a kan boye kayan tallafi korona da ake zarginsu. Hoto daga @Premimutimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Buhari ya sha alwashin daukar mataki a kan bata-gari

A wani labari na daban, Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Legas, Sanai (SOB) Agunbiade ya ce an biya batagarin da suka afka wa gidansa da ke Ikorodu a ranar Juma'a ne, don su kashe shi.

Agunbiade, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ikorodu ta daya, ya ce ya ji kishin-kishin cewa za'a kai masa harin, amma ya zaton duk soki burutsu ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel