Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola

Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola

- Matasa a garin Yola da ke jihar Adamawa sun kai wa ma'adanar kayan abinci na rage radadin korona ziyara

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020

- An ga tarin daruruwan matasa suna kokarin balle kofar ma'adanar domin kwasar kayan abincin da ke ciki

Fusatattun matasa a karamar hukumar Yola ta jihar Adamawa sun garzaya ma'adanar tallafin rage radadin korona na jihar>

Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga matasan suna kokari har ta kai ga sun balle kofar ma'adanar inda suka dinga murna tare da ihu.

KARANTA WANNAN: Sojin saman Najeriya sun kai samame, sun halaka 'yan Boko Haram masu yawa a Borno

Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola
Tallafin korona: Bidiyon matasa suna balle ma'adanar kayan abinci a Yola - @daily_trust
Asali: Twitter

Har ila yau, a cikin bidiyon an ji mai dauka yana sanar da cewa, gwamnatin jihar ta ji abinda ke faruwa amma ta turo jami'ai domin su raba, sai dai basu riga sun iso ba.

Kamar yadda bidiyon da Daily Trust ta wallafa ya nuna, matasan sun kasa jiran jami'an inda suka balle kofar tare da ihun murnar kwasar ganimar da za su yi.

A wani labarin, Kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin 'yan sanda ya ce akwai bukatar a biya diyya ga 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar EndSARS.

An yi zanga-zanga a fadin kasar nan a kan cin zarafi da zaluncin 'yan sanda a fadin kasar nan, lamarin da ya zarta mako daya.

KARANTA WANNAN: Gwamna AbdulRazaq ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m

'Yan Najeriya sun bi tituna inda suke bukatar a gyara ayyukan 'yan sanda amma sai zanga-zangar ta koma wani abu daban.

A yayin jawabi a taron, Mohammed Adamu, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Shugaban kwamitin, Usman Bello Kumo, sun ce diyyar za ta kasance ga 'yan sanda ne da kuma farar hula da suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu.

Kumo ya ce akwai bukatar a fitar da sunayen wadanda suka rasa rayukansu da kuma kadarorin sa aka rasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel