EndSARS: Gwamna AbdulRazaq ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m

EndSARS: Gwamna AbdulRazaq ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m

- Gwamnatin jihar Kwara ta shirya raba N500m ga 'yan kasuwar da bata gari suka balle shagunansu a Ilorin

- Gwamnan jihar AbdulRazaq ya sanar da hakan, yana mai cewa hakan ne kawai zai iya farfado da kasuwancin su, har su tsaya da kafafunsu

- Haka zalika, ya yi Allah-wadai kan yadda bata garin suka sace kayan sana'ar 'yan kasuwar, ya ba da tabbacin gano su tare da yi masu hukunci

Gwaman jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya sanar da cewa zai raba N500m ga 'yan kasuwar da bata gari suka balle masu shaguna ranar Juma'a a Ilorin, birnin jihar.

Ya ce wannan tallafin, na daga cikin kokarin gwamnatin jihar bisa jagorancin sa na ganin cewa ta taimakawa 'yan kasuwar wajen tsayawa da kafafuwansu.

Haka zalika, ya yi Allah-wadai kan yadda bata garin suka sace kayan sana'ar 'yan kasuwar, yana mai ba ta tabbacin cewa za a gano su tare da yi masu hukunci.

KARANTA WANNAN: Kwamitin majalisa na bukatar a biya diyyar mamata

EndSARS: Gwamna Abdulrazak ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m
EndSARS: Gwamna Abdulrazak ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m - @TheNationNews
Asali: UGC

Ya jajantawa 'yan kasuwar da wannan waki'ar ta shafa, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa a ranar Lahadi.

A yayin ziyarar da ya kai Kwara Mall da Agro Mall a yammacin Asabar, gwamnan ya ce aika aikar bata garin na iya durkusar da 'yan kasuwar, da haifar da rashin aikin da talauci.

"Ya zama dole mu tallafawa wadanda 'yan kasuwa, ba zamu iya barinsu haka ba. Za mu raba masu N500m domin ganin sun farfado daga wannan asara da suka yi.

"Yan kasuwa za su cike bukatar samun wannan tallafi a shafin gwamnatin jihar. Za mu raba masu wannan tallafi ba da bata lokaci ba," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Matasa sun cire wa dan sanda kai, sun kashe wasu 3 a Anambra

Ya kuma ce zargin da ake yiwa gwamnatin jihar na boye kayan tallafin COVID-19 ba gaskiya bane, duk kayan da aka sace ba mallakin jihar bane.

A wani labarin, Shugaba Buhari bai ce komai a kan harbe-harben da aka yi a Lekki a ranar Talata ba a jawabin da yayi ga 'yan Najeriya saboda baya son yayi riga Malam masallaci.

Da yawa daga cikin 'yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan rashin maganar shugaban kasan ko jaje ga jama'ar da suka rasa rayukansu. Sun kwatanta hakan da ganganci da kuma rashin nuna kulawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel