Sama da babura 350, firinji 400, janareto, injin nika aka sace a gidana - Sanata Folarin

Sama da babura 350, firinji 400, janareto, injin nika aka sace a gidana - Sanata Folarin

- Sanata Folarin ya yi martani a kan satar da bata gari suka yi a gidansa

- Wasu bata gari sun kai farmaki gidansa a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, sannan suka sace wasu muhimman abubuwa

- Dan majalisar ya bayyana cewa fiye da babura 350 da firinji 400 aka sace daga gidansa

Yan sa’o’i bayan bata gari karkashin inuwar masu zanga-zangar EndSARS sun kai farmaki gidansa tare da yi masa sata, dan majalisa mai wakiltan Oyo ta tsakiya, Sanata Teslim Folarin, ya yi martani.

Channels TV ta ruwaito cewa dan majalisar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa an sace kayayyakin tallafi da suka hada da babura, firinji, injin janareto, inji nika da sauransu fiye da 1,100 a gidansa.

Legit.ng ta tattaro cewa Folarin, wanda ya kuma kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan lamuran cikin gida, ya bayyana cewa wasu bata gari ne suka kai harin.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Ya bayyana harin a matsayin mugunta, jahilci kuma abun bakin ciki, cewa godiyarsa daya da ba a rasa rai ba.

Sama da babura 350, firinji 400, janareto, injin nika aka sace a gidana - Sanata Folarin
Sama da babura 350, firinji 400, janareto, injin nika aka sace a gidana - Sanata Folarin Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Ya ce ya yi amfani da kudinsa wajen siyan karin kayayyaki, inda ya ce ya siyi kayayyakin ne gabannin babban taro na bayar da tallafi da za a yi a watan Nuwamban 2020.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Obasanjo ya jinjina wa jawabin Shugaba Buhari kan zanga-zangar EndSARS

Sanata Folarin ya ce:

“Kayayyakin da aka sace ciki harda babura fiye da 350, firinji 400, janareto 350, injin nika, keken dinki, kayan gyaran gashi na mata da maza, da sauran."

A wani labari na daaban, mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng