Ana harbe harbe a kasuwar Abuja yayin da ƴan sanda suka hana fasa ma'ajiyar abinci

Ana harbe harbe a kasuwar Abuja yayin da ƴan sanda suka hana fasa ma'ajiyar abinci

- Mutane da dama sunji rauni a kokarin gujewa masu yunkurin fasa ma'ajiyar kayyaki a kasuwar UTC a Abuja

- 'Yan sanda suna harba bindiga da barkanon tsohuwa don dakatar da ƴan ta'adda daga fasa dakin adana kayan

- Mazauna yankin Bukuru a Jos suna jidar kayan abinci daga ma'ajiyar kayyaki a jahar Plateau

'Yan kasuwa a kasuwar UTC, Area 10, Garki, Abuja da kuma mazauna yankin suna cike da fargaba yayin da ƴan sanda ke kokarin dakatar da yan ta'adda daga fasa ma'ajiyar kayyaki a yankin.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaro suna ta harba bindiga da barkanon tsohuwa don dakatar da ƴan ta'addan daga fasa ma'ajiyar kayyaki da kayan tallafin Corona ke ciki da sanyin safiyar yau.

Ana harbe harbe a kasuwar Abuja yayin da ƴan sanda suka hana fasa ma'ajiyar kayyaki
Ana harbe harbe a kasuwar Abuja yayin da ƴan sanda suka hana fasa ma'ajiyar kayyaki. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Ma'ajiyar tana nan a yankin Cyprian Ekwensi a kasuwar UTC.

DUBA WANNAN: EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci

Wani mai zane, Segun Stickers, yace an rufe kasuwar UTC da wani babban rukunin shagunan siyayya.

"Yanzu haka muna rufe a cikin kasuwar UTC. Yan sanda suna ta harba bindiga da barkanon tsohuwa don kare mahara daga yunkurin sace kayyakin tallafin Corona a ma'ajiyar dake cikin kasuwar.

"Mutane da dama sun ji rauni a kokarin gujewa maharan, kuma gaba daya yankin suna cikin firgici," ya shaida ta wayar salula.

Wakilanmu suna iya jin karar harbi da kuma murya ana cewa kowa ya rufe shagonsa ya tafi gida.

Mai magana da yawun yan sandan babban birnin tarayya, ASP Mariam yusuf ta tabbatar da cewa an girke yan sandan a kasuwar UTC da sauran wuraren gwamnati don kare aukuwar irin wannan.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba mu raba wa mutane kayan tallafin korona ba - Gwamnatin Osun

Makamancin irin wannan lamarin yana faruwa a Bukuru, Jos South, a jahar Plateau, inda mazauna yankin ke jidar kayyakin tallafin da aka adana.

Wani shaidar gani da ido yayi bayanin cewa daruruwan mutane dake zaune a yankin Bukuru ne ke jidar kayyakin a ma'ajiyar kayyaki dake tsohuwar NITEL kusa da gidan man total, suna diban kayan abinci irinsu buhun shinkafa dana masara wanda gwamnatin jihar ta adana.

Irin wannan lamarin dai ya faru a jahohin Lagos, Osun, Cross river da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel