Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA

Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA

- Majalisar Koli ta shari'a ta kai kuka, ana kaiwa Musulmai hari a kudancin Najeriya

- An kona Masallacin Orlu dake jihar Anambara ranar Laraba

Majalisar Koli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya NSCIA karkashin jagorancin mai alfarma sakrin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, ta bayyana bacin ranta kan rikice-rikicen da ke faruwa a fadin tarayya.

NSCIA ta bayyana cewa abin takaici shine yanzu Musulmai ake kaiwa hari.

Bisa jawabin da shugaban kwamitin yada labaran majalisar, Femi Abbas ya saki, ya bayyana cewa an samu labarin Musulmai a sassa daban-daban na cikin fargaba saboda ana shirin kai musu hari saboda ba Kiristoci bane.

Jawabin ya ce hakan na faruwa musamman yankin kudu maso kudu da kudu maso gabas.

KU KARANTA: Bamu da gidan zama, an hana mu komai na gado - Daya daga matan marigayi Ado Bayero

Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA
Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA
Asali: UGC

"Hadarin haka shine zamu iya shiga wani mumunan rikicin addini, kuma babu wanda ya san yadda zata kare," cewar jawabin.

"NSCIA ta samu bayanin hare-haren da ake kaiwa wurare a yankunan kudu maso kudu da kudu maso gabas."

"Bisa labarin da majalisar ta samu, Musulmai kawai ake kaiwa hari a wadannan yankunan."

"Misali, an kai hari babban Masallacin Orlu a Imo, kuma an kona ta kurmus ranar Laraba, 21 ga Oktoba 2020 kuma an kashe Musulmi daya yayinda hudu sun jikkata."

"Wadanda aka raunata na jinya yanzu a asibiti rai a hannun Allah."

"Kafin harin da aka kai Masallacin, sai da aka kwashe dukiyoyin masu zama a Masallacin."

KU KARANTA: Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a

NSCIA ta ce Najeriya na da matsalolin siyasa da tattalin arzikin da take fama da su, "saboda haka kara samun matsalar addini ba karamin illa zai haifarwa kasar ba."

Ta yi kira ga Sifeto Janar na yan sanda ya dau mataki tun da wuri.

A wani labarin daban, wasu mutane a jihar Calabar sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke Bishop Moynah Street, inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so.

Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel