Dalilin da yasa ba mu raba wa mutane kayan tallafin korona ba - Gwamnatin Osun

Dalilin da yasa ba mu raba wa mutane kayan tallafin korona ba - Gwamnatin Osun

- Kwamitin rabon kayan tallafin korona ta ce tana jiran sahalewa daga Abuja kafin fara raba kayyakin

- Mazauna jihar sun ce basu san dalilin ci gaba da ajiye kayayyakin duk da cewa suna cikin bukata

- Sakataren Kwamitin ya ce akwai ragowar kayyakin da basu zo hannu ba, dalilin da yasa suke ci gaba da ajiyar kayan

Kwamitin rabon abinci da kayan tallafin korona, wanda ke da alhakin rarraba tallafi da Gwamayar kungiyoyi masu yaki da cutar, CACOVID suka bada, a ranar Juma'a, ta bayyana cewa basu raba kayan tallafin bane saboda rashin samun sahalewar wanda suka bada tallafin.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sakataren Kwamitin, Alhaji Bayo Jimoh ya ce kwamitin yana tsammanin sahalewar (CACOVID) kuma ya ce an sace wasu kayayyakin daga ma'ajiyar kayyakin a unguwar Ede.

Dalilin da yasa ba mu raba wa mutane kayan tallafin korona ba - Gwamnatin Osun
Dalilin da yasa ba mu raba wa mutane kayan tallafin korona ba - Gwamnatin Osun. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rayuka 69 suka salwanta sakamakon zanga zanga EndSARS, inji Buhari

Ya ce, "Ba gaskiya bane cewa mun boye kayan abincin. Ba za mu iya rabar da kayan abincin ba har sai an kaddamar da fara rabon a ofishin CACOVID da ke Abuja.

"Bamu da ikon raba kayan ba tare da samun sahalewa daga Abuja ba.

Mazauna jihar sun bayyana cewa an kawo kayyakin ne don a rabawa mutane lokacin da ake zaman gida sakamakon annobar korona amma aka barsu a ma'ajiya.

KU KARANTA: 'Yan daba sun afka wurin da aka ajiye kayan tallafin korona a Osun

Sai dai Bayo ya bayyana cewa kwamiti yana jiran akawo ragowar shinkafa data kai buhu 40,230 masu nauyin kilo gram 5, yana mai cewa, "Wannan duk suna cikin dalilin da yasa kayyakin suke ajiye ba a raba ba har lokacin da aka yi kutsen."

Ya ce, "Ga kayyakin da aka bada tallafin; taliyar FMN 29,992; taliyar OLAM 10,285; kananan taliya 80,6644; garri 40,322; gishiri 40,320 da sukari 40,227.

"Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai ragowar shinkafar da aka bada gudunmawa amma basu karba ba," a cewarsa.

A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel