Rayuka 69 suka salwanta sakamakon zanga zanga EndSARS, inji Buhari

Rayuka 69 suka salwanta sakamakon zanga zanga EndSARS, inji Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mutane 69 ne suka mutu sanadin zanga zangar EndSARS

- Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawar da ya yi da tsaffin shugabanin Najeriya a ranar Jumaa ta hanyar amfani da intanet

- Buhari ya ce wadanda suka mutun sun kunshi farar hula 51, yan sanda 11 da sojoji guda bakwai

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a kalla mutum 69 ne suka rasa rayyukansu a zanga zangar EndSARS da matasa suka yi kwanaki suna yi a jihohin kasar.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, shugaban kasar ya bayyana adadin mutanen da suka mutun ne yayin ganawa da ya yi da tsaffin shugbannin Najeriya ta hanyar amfani da fasahar intanet mai nuna bidiyo da sauti.

Rayuka 69 suka salwanta sakamakon zanga zanga EndSARS, inji Buhari
'Yan zanga zangar EndSARS. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)

An jiyo Buhari na cewa cikin wadanda suka mutu akwai farar hula 51, yan sanda 11 da sojoji guda bakwai.

Buhari ya shaidawa tsaffin shugabannin cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta amsa bukatun masu zanga zangar amma ba zai bari bata garin da suka kwace zanga zangar su cigaba yada barna ba.

KU KARANTA: Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci, in ji Buhari

A halin yanzu an dakatar da zanga zangar a birane da dama a kasar sakamakon dokokin hana fita da wasu gwamnonin jihohi suka sa.

Kazalika, sifeta janar na yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bada umurnin baza jamian yan sandan kwantar da tarzoma zuwa jihohin kasar.

An fara zanga zangar ne tun a ranar 7 ga watan Oktoban da manufar neman gwamnati ta soke rundunar yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami da ake yi wa lakabi da SARS.

A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.

Da ya ke jawabi bayan ya ziyarci wuraren da aka yi rikici a jihar, gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe shida na yamma.

Ya ce za a sake yin bita kan dokar hana fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel