Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita, ya ce ba taba tafka asara irin wannan a tarihin Legas ba

Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita, ya ce ba taba tafka asara irin wannan a tarihin Legas ba

- Gwamnan Legas Babaide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita a jihar

- Gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma

- Sanwo-Olu ya kuma ce gwamnatin za ta sake yin bita kan dokar hana fitar ranar Litinin

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.

Da ya ke jawabi bayan ya ziyarci wuraren da aka yi rikici a jihar, gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe shida na yamma.

Ya ce za a sake yin bita kan dokar hana fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita, ya ce ba taba tafka asara irin wannan a tarihin Legas ba
Babajide Sanwo-Olu. Credit: @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan daba sun afka wurin da aka ajiye kayan tallafin korona a Osun

Gwamnan ya ce bai taba ganin barna irin wanda aka yi cikin 'yan kwanakin nan ba a tarihin jihar Legas.

Amma duk da haka ya mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi don farfadowa da kawo gyara a jihar.

Har wa yau gwamnan ya gargadi mutanen jihar cewa batun zanga zanga ya isa haka.

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (ritaya) ya yi kira ga matasan Najeriya su dakatar da zanga zangar EndSARS don bada daman tattaunawa.

Abdulsalami ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida a Minna akan zanga zangar #ENDSARS da ake yi a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel