'Yan daba sun kashe DCO, sun yi awon gaba da makamai kuma DPO ya bata

'Yan daba sun kashe DCO, sun yi awon gaba da makamai kuma DPO ya bata

- Matasa masu zanga-zanga sun kashe DCO na ofishin 'yan sandan da ke Atan-Ota, DSP Augustine Ogbeche

- Matasan sun banka wa ofishin 'yan sandan wuta inda suka raunata DPO wanda har yanzu ba a san inda yake ba

- A cikin hakan, wani matashi farar hula ya rasa ransa yayin da suke kwashe makamai daga ofishin 'yan sandan da suka saka wa wuta

Fusatattun masu zanga-zanga a ranar Laraba sun kashe babban jami'in binciken laifuka, DSP Augustine Ogbeche tare da banka wa ofishin 'yan sanda na Atan-Ota Ado-Odo da ke karamar hukumar Ota ta jihar Ogun wuta.

Masu zanga-zangar sun raunata DPO na ofishin, SP Sikiru Olugbenga sannan har yanzu ba a san inda yake ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, The Punch ta wallafa.

KU KARANTA: Sojoji sun sheke Abubakar Haruna, dillalin makaman 'yan bindigar Katsina

Oyeyemi ya ce daya daga cikin farar hular masu zanga-zangar ya rasa rayuwarsa yayin da suke kone wani ofishin 'yan sanda da ke Obada-Oko ta karamar hukumar Ewekoro.

Ana amfani da ofishin a matsayin babban ofishin 'yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami.

'Yan daba sun kashe DCO, sun yi awon gaba da makamai kuma DPO ya bata
'Yan daba sun kashe DCO, sun yi awon gaba da makamai kuma DPO ya bata. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ohaneze Ndigbo, babbar kungiyar kabilar Igbo, ta juyawa Nnamdi Kanu baya

Oyeyemi ya ce, "Abun takaici ne yadda zanga-zangar lumana ta matasa a jihar Ogun ta koma rikici. Wasu bata-gari sun yi amfani da damar wurin aikata miyagun laifuka.

"A safiyar Laraba, masu zanga-zangar sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke Atan-Ota inda suka banka masa wuta sannan suka kashe DCO, DSP Augustine Ogbeche.

"Wani farar hula ya rasu sannan sun yi awon gaba da makamai. Sun raunata DPO, SP Sikiri Olugbenga wanda har yanzu ba a san inda yake ba.

"Hakazalika a Abeukuta, wata kungiyar matasa ta kai hari ofishin 'yan sanda na Obada-Oko inda suka tarwatsa ta."

Kakakin rundunar 'yan sandan ya sanar da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Edward Ajogun, ya yi kira ga matasa da su yi watsi da rikicin tare da rungumo zaman lafiya.

A wani labari na daban, a cikin wani faifan bidiyo da ya yi farin jini a dandalin sada zumunta, an ga sojojin Najeriya na lallaba matasa ma su zanga-zanga a jihar Legas.

A daren ranar Talata ne wasu kafafen yada labari na gida da ketare suka wallafa rahoton cewa dakarun soji sun budewa ma su zanga-zanga a yankin Lekki na jihar Legas wuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel