PDP ta shigar da karar INEC da Gbajabiamila bayan jigo a jam'iyyar ya koma APC

PDP ta shigar da karar INEC da Gbajabiamila bayan jigo a jam'iyyar ya koma APC

- Ficewar Honarabul Ephraim Nwuzi daga PDP ta fusata mahukuntan jam'iyyar

- Honarabul Nwuzi ya shiga zauren majalisa ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin mamba a PDP, amma ya fito daga majalisa a matsayin dan APC

- Dan majalisar ya kufula tare da jin haushin dariyar da abokansa 'yan PDP suka yi masa, lamarin da ake zargin ya fusata shi ficewa daga jam'iyyar nan take

Jam'iyyar PDP, ta shigar da ƙarar shugaban majalisar wakilai, Honarabul Femi Gbajabiamila, tare da Honarabul Ephraim Nwuzi, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Etche/Onuma a jihar Rivers.

Bayan 'yan majalisar, PDP ta hada da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa(INEC) sakamakon sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC da Honarabul Nwuzi ya yi a farkon watan Oktoba.

Ɗan majalisa Nwuzi ya sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP a ranar Laraba 7 ga watan Oktoba, 2020 a zauren majalisar, lamarin da ya haifar da hargowa tare da fusata PDP

Jam'iyyar PDP ta shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Port Hacourt a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, kamar yadda takardar kara mai lamba FHC/PHC/CS/159/2020 ta nuna.

KARANTA: Hotuna da bidiyo: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, sun tafka barna

Shari'a ce a tsakanin PDP, dan majalisa Ephraim Nwuzi, shugaban majalisar wakilai, dakuma hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta(INEC).

PDP na neman kotu ta tilasta Gbajabiamila ya bayyana kujerar Honarabul a matsayin 'ta mai rabo' sannan ta umarci INEC ta janye takardar shahadar cin Honarabul Nwuzi saboda sauya sheka zuwa APC ba tare da wani dalili ba.

PDP ta shigar ka karar INEC da Gbajabiamila bayan jigo a jam'iyyar ya koma APC
Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

A cewar PDP, Honarabul Nwuzi bashi da wani uzuri da zai fake da shi a matsayin dalilinsa na fita daga jam'iyyar.

Amma, da jaridar Vanguard ta tuntuɓe shi dangane da lamarin a ranar Alhamis, Honarabul Nwuzi ya ce yana maƙale a jihar Legas sakamakon zanga-zangar kawo ƙarshen rundunar SARS,in da yace har yanzu ba'a sanar dashi an shigar da kararsa ba a hukumance ba.

KARANTA: Baka isa ka hadamu fada da Yarabawa ba: Ohanaeze Ndigbo ta juyawa Nnamdi Kanu baya

A cewarsa; "yanzu nake samun wannan labari daga gareku, banda wata masaniya kafin yanzu domin ba'a sanar dani ba.

''Ina maƙale a jihar Legas a har yanzu saboda zanga-zangar da ke gudana,'' a cewarsa.

Idan zamu tuna baya, rikicin ya samo asali ne a ranar Laraba 7 ga watan Oktoba 2020 lokacin da ƴan mambobin jam'iyyar PDP suka gaida Honarabul Ephraim Nwuzi cikin isgili da tsokana.

A ranar shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila, ya sanar da ficewar Honarabul Nwuzi daga jam'iyyar PDP tare da mara masa baya a kan matakin da ya ɗauka na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel