EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa

EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa

- Gwamonin Arewacin Najeriya sun yi ganawar gaggawa a jihar Kaduna ranar Alhamis

- Gwamnonin sun bukaci yan Najeriya kada su yarda wasu bata gari su durkusar da kasar

Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta bayyana bacin ranta kan wasu bata gari da yan siyasa da suka lashi takobin durkusar da kasar nan da kuma kokarin juyin mulki.

Gwamnonin sun yi mamakin ta wani dalili za'a cigaba da zanga-zanga bayan irin sauraro da biyayyar da gwamnatin tarayya da na jihohi suka yi.

A jawabin da aka saki bayan zaman gaggawan da sukayi a jihar Kaduna ranar Alhamis, gwamnonin sun yi kira ga yan Najeriya su yi fito-na-fito da makiyan Najeriya ta hanyar goyawa shugaban kasa baya.

A cewar jawabin da shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong, ya rattafa hannu, gwamnonin sun tattauna kan matsalolin tsaro da lalata dukiyoyin a sassar kasar.

DUBA NAN: Jerin gidajen yari 5 da aka kai wa hari a yayin zanga-zangar EndSARS

EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa
EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa Hoto: GovKaduna
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya

"Saboda damuwa kan abubuwan dake faruwa, gwamnonin Arewacin Najeriya sun hadu kuma sun tattauna kan lamarin,"cewar jawabin.

"Kungiyar gwamnonin na jajintawa wadanda suka rasa rayukansu, wadanda suka jigata da wadanda sukayi asarar dukiyoyinsu."

"Kungiyar na nuna bacin ranta kan wasu bata gari, masu amfani da addini, kuma yan siyasa da suka lashi takobin durkusar da kasar ta hanyar neman juyin mulki."

"Kungiyar ta yi kira ga yan Najeriya su nuna rashin amincewarsu da wadannan makiyan kasar ta hanyar goyawa shugaban kasa baya."

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wasu 'yan Najeriya suna zaton ragwanci ne gaggawar da gwamnati ta yi na soke rundunar 'yan sanda ta musamman masu yaki da fashi da makami na SARS.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya yi wa kasar kai tsaye a yammacin ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel