EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar

EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar

- Bayan rikicin EndSARS da ya koma tarzoma a yankin kudancin kasar nan, Buhari ya yi jawabi

- Daga cikin jawabinsa ya bayyana damuwarsa a kan yadda wasu bata-gari suka kwace zanga-zangar

- Ya ce 'yan kasa suna da damar zanga-zanga amma ta luamana ba ta tashin hankali da rikici a kasa ba

Bayan mutane sun jima suna jiran martanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayar a kan zanga-zangar EndSARS, da yammacin Alhamis, 22 ga watan Oktoba ya yi jawabi da kuma jawo hankalin al'umma, ga muhimman jawabin na sa.

1. Shugaba Buhari yace duk dan Najeriya yana da damar yin zanga-zangar lumana idan bukatar hakan ta zo, sai dai a tabbatar ba'a shiga hurumin shari'a ba.

2. Wajibi ne duk wani dan kasa ya kiyaye tayar da tarzomar, domin yin hakan ya ci karo da sashi na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya amince da yin zanga-zangar lumana.

3. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki matakin tabbatar da walwalar 'yan sanda. Inda ya umarci hukumar albashi ta kasa da tayi gaggawar amsar sabon tsarin.

4. Shugaban kasa ya bayyana yadda gwamnatinsa ta dauki matakan da za su tabbatar da yaki da talauci. Inda ya lissafo irin tallafin da gwamnati sa ta fara badawa irin Farmer Money, Trader Money, N-Power, N-Agro da sauransu.

6. Ya kara da mika sakon godiyarsa ga kasashen ketare da suka nuna damuwarsu akan zanga-zangar, yayin da ya shawarci kasashen da suka yi alawadai da budewa masu zanga-zangar wuta da sojoji suka yi. Inda yace bai dace su dauki labarin bangare daya ba, ya kamata su tuntuba suji gaskiyar lamarin.

KU KARANTA: Kalaman Fafaroma Francis a kan auren jinsi zasu jawo ma sa suka a duniya

EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar
EndSars: Abu 6 da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa 'yan Najeriya kan zanga-zangar. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga

A wani labari na daban, rahoton da Legit.ng ke samu daga jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa wasu batagari sun kai hari babban ofishin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da ke Akure.

A hotuna da faifan bidiyo da Vanguard ta yada, an ga matasa na kone-kone yayin da suke lalata ofishin da Akeredolu ya yi amfani da shi yayin yakin neman zabensa da aka kammala ranar 10 ga watan da muke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel