EndSARS: Bata-gari ne suka karbe zanga-zangar - Buhari

EndSARS: Bata-gari ne suka karbe zanga-zangar - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunnen matasan da suka canja salon zanga-zangar EndSARS

- Ya ce hakkin dan kasa ne yin zanga-zangar lumana idan hakan ya zama wajibi a garesa

- Amma baya daga kundin tsarin mulkin Najeriya a mayar da zanga-zanga ta'addanci a ko ina

Zanga-zangar EndSARS ta canja salo cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta wallafa.

A jawabin da shugaban kasa yayi da daren Alhamis, wanda ya ja kunnen wadanda suka yi uwa da makarbiya a kan zanga-zangar ya ce lallai gwamnatin tarayya ba za ta yarda da sauran ta'addanci ba.

Yace: "Wajibi ne in ja kunnen wadanda suka canja wa zanga-zangar EndSARS salo daga asalin makasudinta, wadda matasa suka fara a kan dakatar da rundunar SARS.

"Zabin yin zanga-zangar lumana na daya daga cikin hakkokin dan kasa na shashi 40 na kundin tsarin mulkin; amma sai dai damar nan ta zanga-zangar bat ada alaka da yin barin kasa-kasa da dokoki."

KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

EndSARS: Bata-gari ne suka karbe zanga-zangar - Buhari
EndSARS: Bata-gari ne suka karbe zanga-zangar - Buhari. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Bata-gari sun fara fashi har cikin gida, sun balle Shoprite a Legas

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasar Najerya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna damuwarsa a kan harbe-harbe da kashe-kashen 'yan Najeriya da aka yi sakamakon bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan sanda da suka yi a kasar nan.

Ya bayyana hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, The Punch ta tabbatar.

Mataimakin shugaban kasar wanda yace ya samu zantawa da wasu wadanda aka kwantar a asbitoci, ya ce wadanda aka harba ko aka kashe sakamakon zanga-zangar za a tabbatar da an bi musu hakkinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng