ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila

ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila

- Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta maka wani dan majalisa a kotu sakamakon amsar rashawar naira miliyan 1.6

- Dan majalisar, mai suna Egwakhide mai wakiltar mazabar Etsako ta gabas da ta yamma ya amsa rashawar a hannun 'yan kwangilar gina makarantu

- Ya amshi kashi 10 bisa dari na miliyan 16.5 wadda ma'aikatar ayyuka da gidaje suka bai wa mazabarsa don gina azuzuwa 3 a wata makarantar sakandire

Kamar yadda takardar karar ta bayyana, Ehwakhide ya amsa kwangilar gina wani bangare mai azuzuwa 3 a makarantar sakandiren gwamnati ta Fugar, wacce dalibai maza da mata ke karatu, a matsayin aiki cikin ayyukan da zai yi wa mazabarsa a 2018.

Ya nemi a bashi kashi 10 bisa dari na Naira Miliyan 16.5.

Inda ya amshi Naira Miliyan 1.6 daga hannun kamfanin Feola Ventures Nigeria limited Limited, kamfanin da zai yi kwangilar, wanda ma'aikatar ayyuka da gidaje suka bayar.

Laifin da dan majalisar yayi karantsaye da dokar amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba ta bangare na 10 da 19 na laifukan rashawa da makamantansu, sashi na 2000, da yayi magana a kan hakan.

Amma Egwakhide ya musanta hakan. Lauyansa, Samuel Sibiri, ya roki kotu da ta bayar da belinsa kuma lauyan ICPC, Adesina Raheem, bai ki hakan ba. Ya roki kotu ta amince da bayar da belinsa don tabbatar da samun damarsa ta cigaba da zuwa kotu don zaman shari'a.

KU KARANTA: Harbi a Lekki: Osinbajo ya magantu, ya bayyana matakin da FG za ta dauka

ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila
ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

A wani labari na daban, wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun afka gidajen jama'a inda suka dinga ballesu a yankin Surulere da ke jihar Legas. A kalla mazauna yankin biyu ne suka tabbatar wa da jaridar The Cable ta wayar salula.

"Tabbas da gaske ne 'yan fashi suna kawo mana hari yanzu. Sun ballo cikin gidajenmu," daya daga cikin jama'ar ya sanar yayin da ake jin harbin bindiga.

A ranar Laraba, jihar Legas ta fuskanci hauhawar rikici inda 'yan daba suka dinga bankawa manyan wurare da ofisoshin 'yan sanda wuta. Manyan kantuna da wuraren saide-saide ba a kyalesu ba a fadin jihar.

Jaridar The Cable ta gano cewa matasan sun fada babban kantin Shoprite da ke yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel