Fursunoni sun bankawa gidan yari wuta a Warri, da dama sun tsere duk da harbe-harben jami'an tsaro

Fursunoni sun bankawa gidan yari wuta a Warri, da dama sun tsere duk da harbe-harben jami'an tsaro

- Mazauna gidan yarin Okere sun tayar da bore tare da tashin gobara a wani yanki na ginin gidan

- Kakakin rundunar NCS ta ce basu da tabbacin ko wani fursuna ya gudu, sai dai jama'a sun ce fursunoni da dama sun tsere

- Fusatattun matasa dauke da adduna da tayoyi sun tayar da sabon rikici a karamar hukumar Warri da ke jihar Delta

Fursunoni sun saka wuta a wani bangare na gidan yarin Warri da ke kan titin Okere a jihar Delta, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta kasa (NCS), DSP Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kara da cewa mahukuntan gidan yarin ba su da masaniyar ko wani Fursuna ya tsere.

"Sun tashi wuta a cikin yarin, amma daga waje lafiya kalau, ba wata matsala. Akwai 'yan sanda a bakin kofa. Ba zamu iya tabbatar da tserewar kowa ba. Wannan shine bayanin da zan iya baku a halin yanzu, idan mun samu wani daga baya zan sanar da ku," a cewarta.

DUBA WANNAN: A karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki alfarma wurin matasa

Sai dai, jaridar The Nation ta rawaito cewa wasu Fursunoni da ba a san adadinsu ba sun tsere daga gidan yarin na Okere duk da harbe-harben da jami'an tsaro ke yi.

Fursunoni sun bankawa gidan yari wuta a Warri, da dama sun tsere duk da harbe-harben jami'an tsaro
Turnukun hayaki daga gidan yarin Okere
Asali: Twitter

Ba a hango komai daga nesa da gidan yarin sai bakin hayaki mai dauke da hucin wuta da ya mamaye yankin ginin gidan, lamarin da ya jefa tsoro cikin zukatan makwabtansu.

DUBA WANNAN: Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo

Jaridar ta rawaito cewa mazauna birnin Warri sun rufe shagunansu tare da guduwa zuwa gidajensu bayan wasu fusatattun matasa dauke da adduna da tayoyi sun fara kone-kone.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun nufi gidan yarin gadan-gadan domin balle shi, kamar yadda wasu matasa suka yi a jihar Edo ranar Litinin.

A wani faifan bidiyo da bai yi kyan nada ba, za a iya ganin matasa na jefa duwatsu zuwa bakin kofar shiga gidan yarin.

Daga bisani an hangi matasan na shewa da murnar jin dadi yayin da wasu fursunoni suka fito suka shiga cikinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng