EndSARS: FG ta kara tura dakarun soji domin tsare kayan gwamnati a Legas

EndSARS: FG ta kara tura dakarun soji domin tsare kayan gwamnati a Legas

- An ninka matakan tsaro don kula da dukiyoyin gwamnati a jihar Legas, cewar gwamna Sanwo-Olu

- Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata hira da gidan talabijin din Arise wanda aka yi da shi a yau

- Ya ce a ranar Laraba shugabannin tsaro biyu ne suka tambayeshi idan yana bukatar karin jami'an tsaro, ya amince

Don gujewa cigaba da asarar dukiyar gwamnati a jihar Legas, gwamnatin tarayya ta kara yawan jami'an tsaro don kula da dukiyoyin gwamnati da ke jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a safiyar Alhamis, yayin da ake hira dashi a gidan talabijin din Arise wanda The PUNCH suka dauka.

Sanwo-Olu yace shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Olonisakin da shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, sun kira shi a waya ranar Laraba.

Yace manyan shugabannin tsaron sun tambayeshi idan yana bukatar karin jami'an tsaro don kulawa da dukiyoyin gwamnati da ke jiharsa, ya amsa su da, "Mai zai hana? Wajibi ne a kula da tashoshin jiragen sama da sauran gine-ginen gwamnati."

Labaran yadda 'yan ta'adda suka yi ta lalata dukiyoyin gwamnati a jihar Legas ya yadu cikin kankanin lokaci.

Sakamakon hakan ne Sanwo-Olu ya saka kullen awanni 24 a jiharsa.

KU KARANTA: Da duminsa: NECO ta dakatar da jarabawa, ta umarci ma'aikata su koma gida

EndSARS: FG ta kara tura dakarun soji domin tsare kayan gwamnati a Legas
EndSARS: FG ta kara tura dakarun soji domin tsare kayan gwamnati a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato ya yi taro da shugabannin gargajiya a gidan gwamnatin Filato don kawo karshen tarzomar da ta barke a jihar, Pemium Times ta wallafa hakan.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya cewa shugabannin gargajiya, su zai kama da laifi matsawar ba'a samu kwanciyar hankali ba a jiharsa sakamakon zanga-zangar rushe SARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel