Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo

Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo

- Har yanzu ana cigaba da samun rfahotannin kai hare-hare a kan gine-gine mallakar gwamnati da daidaikun jama'a

- Hakan na cigaba da faruwa duk da an sanar da saka dokar ta baci a kusan jihohin Najeriya takwas

- Ana zargin cewa wasu batagari sun kwace iko da zangar-zangar lumana ta neman a rushe rundunar SARS da matasa suka fara kimanin sati biyu da suka gabata

Rahoton da Legit.ng ke samu daga jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa wasu batagari sun kai hari babban ofishin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da ke Akure.

A hotuna da faifan bidiyo da Vanguard ta yada, an ga matasa na kone-kone yayin da suke lalata ofishin da Akeredolu ya yi amfani da shi yayin yakin neman zabensa da aka kammala ranar 10 ga watan da muke ciki.

DUBA WANNAN: A karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki alfarma wurin matasa

Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo
Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo
Asali: Twitter

Da sanyin safiyar ranar Laraba ne sojoji suka isa 'Douglas House' bayan dokar ta bacin da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya saka ta fara aiki, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Dakarun rundunar soji sun mamaye hanyoyin shiga gidan gwamnatin jihar Imo, 'Douglas House'.

Sojojin sun yi hakane domin hana fusatattun ma su zanga-zanga samun damar shiga gidan.

DUBA WANNAN: 'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga

Dandazon masu zanga-zanga sun yi tururuwar fitowa domin cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da sanarwa da gwamna Uzodinma ya fitar da yammacin ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamna Uzodinma ya fitar da sanarwar a kurarren lokaci.

Yawanci mazauna jihar, da suka hada da daliban da ke zuwa makaranta, basu san an saka dokar ta baci ta 24 ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel