Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

Kamar yadda jaridar ThisDay ta wallafa, an ji harbe-harbe tare da ganin mummunar wutar gobara ta tashi a gidan gyaran hali da ke Ikoyi a jihar Legas.

Hakan baya rasa alaka da rikicin tare da tarzomar da ta barke a jihar tun daga zanga-zangar EndSARS.

Jami'an 'yan sanda da sojoji sun isa gidan gyaran hali da ke Ikoyi a kokarinsu na datse yunkurin balle gidan da aka yi.

Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga hayaki na fitowa daga wasu sassan gidan yarin yayin da 'yan gidan ke gudu domin neman wurin zuwa.

An gano cewa, hukumomin gidan gyaran halin sun gaggauta sanar da 'yan sanda da sojoji domin daukar matakin da ya dace.

Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta
Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ganau ba jiyau ba wanda ya bukaci da a boye sunansa ya ce, "Ina kallo ta baya yadda sojoji da 'yan sanda suka isoo. Na ga 'yan gidan yarin suna jifansu da duwatsu kuma na ga wuta tana tasi.

"Da yawa daga cikin jami'an sun taru a hanyar shiga gidna gyaran halin yayin da 'yan gidan yarin suka koma baya."

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya ce har yanzu ba san abinda ya kwo wutar ba amma 'yan sanda sun mamaye gidan.

"Ba mu san abinda ya kawo gobarar ba amma jami'anmu suna wurin. Za mu bada karin bayani nan babu dade," yace.

Karin bayani na na tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel