Coronavirus: An samu adadin sabbin masu kamuwa mafi karanci cikin watanni 8 a Najeriya
- Kwanaki biyu kenan hukumar NCDC ta daina sakin adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar Korona
- Premium Times ta bayyana cewa ta samu adadin da wajen NCDC amma hukumar bata wallafa a shafukanta ba
Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus mafi karanci cikin watanni takwas a ranar Laraba inda mutane 37 kacal suka kamu da cutar, a cewar hukumomin kiwon lafiya.
Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 61,667 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Laraba, 21 ga watan Oktoba, 2020, Premium Times ta ruwaito.
Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 61,000 da suka kamu, 56,880 sun warke.
A cewar NCDC, mutane 3,662 ke jinya yanzu.
Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu– FCT (8), Lagos (7), Taraba (5), Rivers (5), Adamawa (4) Kaduna (3), Anambra (2), Osun (2), Ogun (1).
KU KARANTA: Jerin wurare 23 da bata gari suka kai hari ko bankawa wuta

Asali: Twitter
KU KARANTA NAN: Fusatattun matasa sun kwace jirgin saman 'yan sanda
A bangare guda, majalisar wakilan tarayya a Najeriya ta kai ga fara binciken zargin badakala a ma’aikatar NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta.
Jaridar Punch ta ce ‘yan majalisar su na binciken wasu makudan kudi har Naira biliyan 6.2 da ake zargin an yi awon gaba da su a NDDC.
Ana zargin an karkatar da wadannan kudi da aka ware domin bada tallafin COVID-19 a yankin.
Bayan nan kuma majalisar wakilai ta na kuma binciken barnar Naira biliyan 139.317 da ofishin mai binciken kudi na kasa ya ke ikirari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng