Sarauniya Amina: Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita

Sarauniya Amina: Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita

- Babu shakka kasar Zazzau ta taba samun wata jarumar Basarakiya da ake kira da sarauniya Amina

- Ta jagooranci maza zakakurai kuma dakarun yaki har 20,000 bayan watanni da hawanta karagar mulki

- Sarauniya Amina gagarumar basarakiya ce da ta kwashe shekaru 34 tana mulki kuma ta fadada arzikin masarautarta

Idan har za a yi zancen mata jarumai a Najeriya, ba za a taba mantawa da sarauniya Amina ta Zazzau ba. Jarumar basarakiyar ta jagoranci rundunar yaki ta maza kuma ta kwato yankuna da yawa a kusa da kasar Zazzau.

Kamar yadda rahoto ya nuna, basarakiyar an haifeta a gidan hamshakin basarake, Sarki Bakwa na Turunku a shekarar 1533 kuma a Zazzau suka rayu.

Gidansu manyan masu arziki ne domin su ke siyar da tufafi, gishiri, goro, karfe da kuma dawakai.

A zamanin mahaifinta, Amina tana samun horon yaki daga sojojin Zazzau, hakan ne ya gogar da ita sosai wanda daga baya ta zama shugaban mayakan.

KU KARANTA: Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump

Sarauniya Amina: Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita
Sarauniya Amina: Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita. Hoto daga Tumblr.com
Asali: UGC

Sarki Bakwa na Turunku ya rasu a 1566 kuma dansa Karama shine ya gajesa. Ya rasu bayan kwashe shekaru 10 yana mulki.

A zamanin Karama, Amina ta zama fitacciyar mayakiya kuma ta zama sarauniya bayan rasuwarsa.

Sarauniya Amina ta jagoranci mayakanta a karon farko bayan watanni kadan da zamanta sarauniya. Ta yi wa dakaru kusan 20,000 jagora zuwa yaki.

Jarumar sarauniyar ta samowa masarautarta arziki mai tarin yawa domin ita ta fara yi wa mayakanta sulken yaki.

Sarauniya Amina bata taba aure ko haihuwa ba. Kamar yadda Face 2 Face Africa ta wallafa, tana kwanciya da mazan da ta samo matsayin ganima sannan sai ta kashesu washegari domin tsare sirrinta.

Ta kashe kanta ne bayan da ta kwanta da wani mutumi amma yayi nasarar tserewa washegari. Jama'a suna kwatanta da mace mai kamar maza.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

A wani labari na daban, daya daga cikin manyan sarakunan kasar nan, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya cika shekaru 82 a duniya kuma daya daga cikin matansa ta shirya masa shagali.

Baya ga murnar, matansa sun shirya masa gagarumar liyafa. Bidiyon liyafar ya karade kafafen sada zumuntar zamani.

Daya daga cikin matansa, Olori Memunat ce ta wallafa bidiyon basaraken yana rawa a liyafar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel