Gwamnatin Jihar Plateau ta saka dokar hana fita a Kananan hukumomi biyu

Gwamnatin Jihar Plateau ta saka dokar hana fita a Kananan hukumomi biyu

- Gwamnatin Jihar Plateau ta saka dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa

- Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a wasu sassan kanananan hukumomin ne yayin da matasa suka fara zanga-zangar EndSARS

- Gwamnan ya ce dokar za ta fara aiki daga karfe takwas na ranar Talata har zuwa wani lokaci nan gaba

Gwamnan Plateau Simon Lalonga ya kafa dokar hana fita ta awa 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu sakamakon ballewar rikici na zanga-zangar EndSARS a jihar.

Da ya ke yin jawabi a yammacin ranar Talata, gwamnan ya ce dokar hana fitar za ta fara aiki daga karfe 8 na dare har zuwa wani lokaci nan gaba.

Gwamnatin Jihar Plateau ta saka dokar hana fita a Kananan hukumomi biyu
Gwamna Simon Lalong: Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

Da ya ke tabbatar da mutuwar mutum uku yayin zanga-zangar, gwamnan ya ce saboda haka an haramta duk wata irin zanga-zanga a jihar.

Mista Lalong ya ce: "Bayan samun rahotanni daga hukumomin tsaro da yin nazari kan lamarin, gwamnati ba ta da wani zabi da ya wuce saka dokar hana fita don kare cigaba da asarar rayuka da dukiyoyi.

"Na bada umurnin saka dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu daga karfe 8 na yau Talata 20 ga watan Oktoban 2020 har zuwa nan gaba. Da wannan umurnin, duk wani nau'in zanga-zanga a kananan hukumomin biyu ya haramta," in ji shi.

KU KARANTA: EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

Mista Lalonga ya kuma umurci dukkan kamfanoni da 'yan kasuwa su rufe kasuwancinsu yayin da ya shawarci iyaye su ja kunnen yaransu, matasa don kare rushewar doka da oda.

"Wadanda ke gudanar da muhimman aiki kawai za su fita zuwa wurin ayyukansu," kamar yadda gwamnatin ta bada umurni.

"An bukaci hukumomin tsaro su tabbatar an bi dokar kuma duk wanda aka samu suna saba dokar za a kama su a gurfanarsu da su gaban doka," ya kara da cewa.

A wani labarin, Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isah Ali Pantami, ya bayyana cewa dole ne matasan Najeriya su maida hankali wajen koyon sana'a kuma su dena dogora ta shaidan kamalla karatu zalla.

Kamar yadda ya bayyana, 'yan Najeriya sunfi maida hankali ga samun shaida ta karatu fiye da koyon sana'o'i, ya kuma kara da cewa akwai sana'o'i da dama a kasar nan sai dai kuma rashin maida hankali a koyi sana'o'in ya sanya ba a cike guraben ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel