An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga

An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga

- Zangar-zangar lumana da aka fara domin neman a rushe rundunar SARS ta rikide zuwa rikici a sassan Nigeria da suka hada da Abuja

- Sakamakon hakan ne babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin baza wasu jami'ai na musamman a fadin kasa

- Ana zargin ma su zanga-zanga da tafka barna, su kuma ma su zanga-zanga na zargin an yi hayar batagari don su bata musu zanga-zanga

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, a ranar Talata, ya bayyana cewa an kama mutane 12 da ake zzargin da hannunsu a kai hari tare da kone wani ofishin 'yan sanda a Benin, jihar Edo.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda na kasa (FPRO), Mista Frank Mba, ya fitar, ya bayyana cewa an samu bindigu kirar AK47 guda biyar da aka sace daga ofishin da aka lalata.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga

IGP Adamu ya bada umarnin gaggauta tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati da na jama'a a fadin kasar nan.

An kama mutane 12 da ake zargi da kone ofishin 'yan sanda yayin zanga-zanga
IGP Mohammed Adamu
Asali: Twitter

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske zuwa ga cibiyoyin kula da masu laifi da ke fadin Kasar.

DUBA WANNAN: Yaro mai shekara 13 ya fado daga babbar mota ya mutu nan take yayin zanga-zanga

Umarnin na zuwa ne biyo bayan karuwar lalata kayayyakin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane da ke faruwa a wasu jihohin kasar da ma birnin tarayya, Abuja.

"Bugu da kari, kwamishinonin yan sanda a jihohi 36 na Najeriya da birnin tarayya, Abuja, za su yi aiki don ganowa tare da ware ɓata gari daga cikin masu zanga zangar lumana. za a kama masu barna tare da ladabtar gurfanar dasu," a cewar sanarwar.

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zangar ENDSARS ya sanar sa janye hannunsa sakamakon sauyawar salon zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng