Da duminsa: An soke dukkan sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas

Da duminsa: An soke dukkan sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas

- Bayan gwamnatin jihar Legas ta sanar da saka dokar ta baci a jihar ta sa'o'i 24, an soke sauka ko tashin jiragen sama

- Kamar yadda al'amuran suka bayyana, an samu nakasar kaiwa da kawowa a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala

- Amma an shawarci matafiya da su sauya ranar tashi ko sauka a jihar tunda dokar ta sa'o'i 24 ce

Bayan saka dokar ta baci a jihar Legas na sa'o'i 24, an soke dukkan tashi ko saukar jiragen sama a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar ta bacin ta sa'o'i 24 sakamakon yadda zanga-zangar lumanar da matasa suka fara ta koma tarzoma a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an durkusar da dukkan kaiwa da kawowa a babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke Legas, sakamakon yadda masu zanga-zangar suka mamaye titin zuwa filin jirgin.

Amma kamfanin jiragen sama na Arik Air ya bada takardar sanarwa inda ya ce ya soke dukkan tashi da saukar jiragensa a garin Legas na ranar Laraba.

Dukkan fasinjojin za su iya soke tashi ko saukarsu a garin kuma ana shawartarsu da su sauya wata rana ba tare da an kara musu wasu kudi a kai ba.

Kakakin kamfanin jiragen sama na Arik, Ola Adebanji ya tabbatar.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

Da duminsa: An dakatar da sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas
Da duminsa: An dakatar da sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas. Hoto daga @DailyTrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Legas ta umarci duk daliban jihar, na makarantar gwamnati da ta kudi, da su zauna a gida saboda tarzomar da masu zanga-zangar rushe SARS suka tayar.

Kwamishinan ilimi ta jihar, Folasade Adefisayo, wacce ta bayar da wannan umarnin, tace don tabbatar da lafiyar dalibai, malamai da kuma iyayen yara, wajibi ne su dakatar da zuwa makarantu a wannan lokacin na tsanani.

Ta kuma shawarci iyaye da su saka ido akan yaransu, don kada ayi amfani da su wurin tayar da hankalin al'umma, The Nation ta wallafa.

Kamar yadda Adefisayo ta ce, jihar Legas zata sanar da lokacin da za'a bude makarantu nan ba da jimawa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel