Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata

Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata

- Masu zanga zangar #EndSARS a garin Waru, gundumar Apo, birnin tarayya Abuja, sun kashe wani mutumi ta hanyar dukansa da katagon 2-by-2

- Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa, masu zanga zangar sun lalata dukiyoyi da kudinsu ya haura miliyoyin Naira

- Sai dai, dakarun soji da na 'yan sanda sun dira garin Waru domin kwantar da tarzoma da kuma cafke wadanda suka tayar da hatsaniyar

Akalla mutum daya ya mutu yayin da aka jikkata mutane da dama a ranar Talata, biyo bayan barkewar sabuwar zanga zangar #EndSARS a gundumar Apo, birnin tarayya Abuja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a yayin zanga zangar da ta barke da misalin karfe 8 na safiya.

Wasu mazauna garin Waru, sun bayyana cewa masu zanga zangar sun aikata wannan mummunar ta'asar ne da sunan nuna rashin goyon baya kan cin zarafin da 'yan sanda ke yiwa jama'a.

KARANTA WANNAN: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos

Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata
Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata - HumAngle
Asali: UGC

Sai dai, tawagar dakarun soji da na 'yan sanda sun durfafi Waru, inda ake hango tashin hayaki da ya turnuke sararin samaniya da misalin karfe 11:15 na safiya domin kwantar da tarzoma.

Haka zalika jami'an tsaron sun datse wasu hanyoyi da ke sada mutane zuwa garuruwan da ake rikicin.

KARANTA WANNAN: AGF ya amince a sallami jami'an SARS 35, kuma a yi masu hukunci

Da ya ke zantawa da jaridar Vanguard, wani da lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce sai da aka gargadi mutumin da ya mutu akan kada ya je Waru saboda akwai yan ta'adda a cikin garin.

"Sai da muka gargadi mutumin da aka kashe da kada ya karasa Waru. Daga nesa muna ganin yadda yan ta'addan suka kashe shi.

"Sun yi amfani da katako '2-by-2' suka rinka dukansa, yana faduwa kasa, suka tumurmusa shi har sai da suka tabbatar ya daina numfashi.

"Rundunar soji da na 'yan sanda sun shiga garin Waru domin kwantar da tarzoma, amma ina da tabbacin cewa, da zaran sun bar garin, rikicin zai sake barkewa," a cewar sa.

Sakamakon wannan mummmunan yanayin, majiyar ya shaida cewa da yawan mata da kananan yara suka gudu daga garin, domin tsira da rayukansu.

A wani labarin, Rundunar soji ta ce za ta fara sabon atisayen murmushin kada a fadin Nigeria. 4

Atisayen kamar yadda ya ke a al'adance, ana gudanar da shi ne a karshen watanni uku na kowacce shekara.

A ranar Asabar ne, 17 ga watan Oktoba, Sagir Musa, mukaddashin shugaban hulda da jama'a na rundunar, ya ce za a fara atisayen a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel