Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

- Jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun mamaye wasu manyan tituna a Abuja

- An gansu a yankunan Kuje, Soka da wasu sassa na Lugbe da ke birnin tarayya

- Jami'an tsaron suna bai wa filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja kariya

Sojoji da 'yan sanda a sa'o'in farko na ranar Talata sun mamaye wasu yankuna da ke da kusanci da filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke garin Abuja.

Zai yuwu an yi hakan ne domin gujewa rikici da barnar masu zanga-zangar bukatar kawo karshen runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami na 'yan sandan Najeriya.

An gan su sun mamaye yankunan Kuje, Soka da wasu sassa na Lugbe, The Punch ta ruwaito.

Wadannan yankunan sun hada da babbar hanya ta Shehu Yar'Adua wacce ke hade da filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja.

A ranar Litinin, masu zanga-zangar sun mamaye titunan kafin daga bisani 'yan daba su mamaye yankin kuma su fatattakesu.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu

Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja
Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun bayyana matakai 5 da suke dauka a kan EndSARS

A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasan Najeriya akan kada su keta iyakar tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS duk da gwamnatin tarayya ta fahimci manufarsu.

Magashi yayi wannan kiran ga matasa a wata takarda da kakakin ma'aikatar, Mohammad Abdulkadri ya saki, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Ma'aikatar ta yi wannan jan kunnen a lokacin da shugaban kamfen din Buhari, Danladi Pasali, ya jagoranci wakilai a ma'aikatar tsaro dake Abuja.

Ministan ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai nagarta, kuma yayi godiya ga kwamitin kamfen din akan dagewarsu wurin ganin cigaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel