Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe

Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe

- I stand With Buhari za ta gudanar da wani babban tattaki a Ranar Laraba

- Kungiyar ta I stand With Buhari ta ce ta na nan tare da gwamnatin Buhari

- A daidai wannan lokaci wasu na fama da zanga-zangar #EndSARS a kasar

Wata kungiya mai suna ‘I stand With Buhari’, ta sanar da shugaban ‘yan sandan Najeriya a garin Abuja, shirinta na gudanar da tattaki na musamman.

Wannan kungiya za ta tara mutane miliyan goma da su fito domin nuna cikakkiyar goyon-bayansu ga tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban wannan kungiya, Ogochukwu Ezeaku, ya shaidawa jaridar Punch wannan a lokacin da aka yi hira da shi a ranar 19 ga watan Oktoba, 2020.

KU KARANTA: ‘Yan iska sun tasa Garin Benin a gaba, sun kona ofishin ‘Yan Sanda

Mista Ogochukwu Ezeaku ya bayyana cewa su na sa ran za su samu goyon-bayan dakarun ‘yan sanda wajen shirya wannan tattaki a birnin tarayya.

Ezeaku ya ce za su fara wannan tafiya ne daga Unity Fountain, a Maitama a ranar Larabar nan.

Da aka tambaye shi ko za a samu sabani tsakaninsu da masu zanga-zangar #EndSARS, Ezeaku ya ce ya san masu fafatukar #EndSARS ba su tada rikici.

Ya ce makasudin wannan tattaki shi ne a nuna wa Duniya cewa akwai dinbin mutanen da ke goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari har gobe.

KU KARANTA: Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar #EndSARS su sassauta

Kungiya ta shirya taron ‘Yan Buhari na mutum Magoya miliyan 10 a Abuja gobe
Kungiyar I stand With Buhari Hoto: facesinternationalmagazine.org.ng/?p=134128
Asali: UGC

Wannan kungiya ba ta kishiyantar masu zanga-zangar #EndSARS, kamar yadda ta bayyana.

‘I stand With Buhari’ ta ce za ta goyi bayan wancan tafiya ta kiran inganta sha’anin tsaro, muddin masu zanga-zangar ba su saki layi, sun koma takalar fada ba.

A jiya ne jam’iyyar APC ta ce akwai lauje cikin nadi a tafiyar #EndSARS. Shugaban APC, Mai Mala Buni ya ce akwai makarkashiya a zanga-zangar da ake ta yi.

Gwamnan na Jihar Yobe ya ce tsageru masu laifi ne ke jin tsoron Dakarun SARS da aka rusa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel