Yanzu yanzu: Sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19, mutane 1125 sun mutu
Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC), ta tabbatar da cewa sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba 2020.
Hukumar NCDC a shafinta na Twitter @NCDCgov, a daren ranar Litinin, ta wallafa cewa jimillar mutane 61558 ne suka kamu da cutar, yayin da mutane 56697 suka warke.
Sai dai hukumar ta wallafa cewa, mutane 1125 ne Allah ya karbi rayuwarsu sakamakon yin jinya na wannan cuta.
KARANTA WANNAN: Na haramtawa 'yan sanda sanya shingen bincike a titunan jiha ta - Gwamna Umahi
Ga dai jaddawalin jihohin da aka samu bullar cutar a wannan rana:
Lagos-51
Rivers-26
Imo-12
Osun-8
Plateau-6
FCT-5
Kaduna-4
Ogun-3
Edo-2
Niger-1

Asali: Twitter
A wani labarin, Tauraron dan wasan Brazil, Neymar ya aika da sakon jaje ga Cristiano Ronaldo, bayan da labari ya fita na cewar Ronaldo ya kamu da cutar COVID-19 a ranar Laraba.
Hukumar kula da kwallon kafar Portuguese (PFF) a jiya ta sanar da cewa Ronaldo na killace a gidansa, kuma zai rasa wasan ranar Laraba tsakaninsu da Sweden a gasar NL.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng