Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina

Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina

- Alkalin babbar Kotun tarayya ta Abuja, Okong Abang, ya bai wa Sanata Ali Ndume kwanaki 21 don ya gabatar da Abdulrasheed Maina a kotu

- Tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina na fuskantar kotu, ya ki bayyana a gaban kotu na kusan zama na 10 tun bayan belinsa

- Ndume yayi dana-sanin tsayawa Maina a kotun, inda ya sanar da kotu cewa bai sake ganin Maina ba, kuma ya amince kotu ta kamo Maina

Babbar Kotun tarayya ta Abuja ta bai wa Sanata Ali Ndume kwanaki 21 don ya gabatar da tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina a ranar Litinin, wanda kusan karo 10 kenan bai je shari'a kotun ba tun watan Satumba 2020.

Mai shari'a Okon Abang, ya bai wa Ndume kwanakin ne, wanda shine tsayayyen da Maina ya gabatar wa kotun, don matsawar bai gabatar da wanda yake karewa ba a kotu ranar 18 ga watan Nuwamba, kotu za ta damke shi.

Daga EFCC har Ndume sun roki kotu da ta bada damar damko Maina a ranar Litinin, jaridar Punch ta ruwaito.

Amma alkalin yace ba zai sa a damko Maina ba, ba tare da rike tsayayyensa ba a hannu.

Yace zai bai wa Sanata damar wasu satittuka don nemo wanda yake karewa ya kuma gabatar da shi a kotu.

Duk da Maina bai gabata a kotu ba, masu mara masa baya sun ce Alkalin na kokarin shafa masa bakin fenti tare da nuna son kai a kotun.

Duk da wani bidiyon Maina yayi ta yawo a yanar gizo, inda Maina ke sanar da jinyar da yake yi ta kafarsa, kuma yace ba zai bayyana gaban kotu ba har sai likitoci sun tabbatar da lafiyarsa.

KU KARANTA: Neymar: Dan wasan kwallon kafan da ya mallaki motoci na N2bn (Hotuna da Bidiyo)

Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina
Zargin damfara: Kotu ta bai wa Sanata Ndume kwana 21 ya kawo Maina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya kori shugaban hukumar hakkin mallaka

A wani labari na daban, an dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Kamar yadda rahoton yazo, "Mun samu labarin yadda aka kama daliban babbar makarantar Loreto da aka dakatar saboda kama su da aka yi suna lalata, duk da ba'a kamasu turmi da tabarya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel