Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga

Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga

- Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa

- Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS

- A yayin da matasa ke cigaba da zanga-zanga, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, da ya tabbatar da tsaron lafiyar ma su zanga-zangar lumana ta neman a kawo karshen rundunar SARS.

Kazalika, shugaba Buhari ya jaddada cewa matasan na da ikon bayyana rashin gamsuwarsu ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana.

Sai dai, shugaba ya yi kira ga matasan a kan su bawa gwamnati lokaci domin duba bukatunsu da tuni aka kafa kwamiti na musamman domin yin hakan.

KARANTA: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya fadi manufar ma su zanga-zanga

Ministan harkokin matasa da wasanni, Sunday Dare, ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da shugaba Buhari a Villa.

Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga
Shugaba Buhari
Asali: UGC

Ministan ya ziyarci shugaba Buhari ne domin yi masa cikakken bayani a kan zanga-zangar da ta kara karfi ranar Litinin.

A cewar, Dare, shugaba Buhari ya sanar da shi cewa shine uba wurin dukkan matasan kasar nan, kuma ba zai so wani abu ya cutar dasu ba.

KARANTA: NPF ta fitar da jawabi a kan arangamar da ma su zanga-zanga suka yi da juna a Abuja

Shugaba Buhari ya ce alhakinsa ne ya kare matasa masu zanga-zanga daga cin zalin 'yan sanda.

Dare ya ce shugaba Buhari ya bashi tabbacin cewa ya saurari korafin matasan kuma zai share musu hawaye.

Ministan ya ce ya gabatar da jawabi ga Buhari a gaban shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, kamar yadda jaridar The Sun ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel