Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos

Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos

- Wasu batagari da ake zargin yan daba ne sun kaiwa jami'an yan sandan RRS hari a jihar Lagas

- Lamarin ya afku ne a yau Litinin, 19 ga watan Oktoba

- Yan iskan sun yi zargin cewa an turo jami'an ne domin su dakatar da zanga-zangar kawo karshen SARS da ake gudanarwa

Wasu yan daba a ranar Litinin, sun kai hari kan jami’an rundunar yan sandan RRS a jihar Lagas.

Harin ya gudana ne a hanyar Herbert Macaulay, da ke yankin Yaba a jihar.

Ana ta samun barkewar rikici a wasu yankunan kasar yayinda ake tsaka da zanga-zangar #ENDSARS.

A cewar wani idon shaida, yan iskan sun farma jami’an tsaron kan hasashen cewa an turo su ne domin su dakatar da zanga-zangar.

Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos
Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

An gano yan daban suna wurgin motocin tawagar ta RRS da duwatsu da sanduna yayinda jami’an suka tarwatse domin neman mafaka.

KU KARANTA KUMA: Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja

Mutuwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, bai amsa kiran da aka masa ba don jin ta bakinsa game da lamarin.

A ranar Alhamis da ta gabata, yan iska sun farma masu zanga-zangar a kofar majalisar dokokin jihar da ke Ikeja.

Lamarin ya yi sanadiyar raunata masu zanga-zanga da dama.

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Edo ta sanar da sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Sabbin mutane 133 sun kamu da Korona, mutane 2 sun mutu nan take

Dokar za ta fara aiki daga karfe 4:00pm na ranar 19 ga watan Oktoba, har sai baba-ta-gani. Babban sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie ne ya fitar da sanarwar, Channels TV ta ruwaito.

Ogie ya bayyana cewa an sanya takunkumin ne sakamakon hare-haren da wasu yan iska da suka mamaye zanga-zangar #ENDSARS suka aiwatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel