Da duminsa: Bidiyon yadda batagari su ka balle gidan yari suka saki ma su laifi a Benin

Da duminsa: Bidiyon yadda batagari su ka balle gidan yari suka saki ma su laifi a Benin

- Wasu gungun batagarin matasa sun balle wani gidan yari da ke kan hanyar Sapele a birnin Benin na jihar Edo

- Matasan sun saki kusan dukkan ma su laifin da ke tsare a gidan yarin

- Balle gidan yarin na zuwa ne a daidai lokacin da zanga-zangar neman rushe SARS ke kara zafi a Benin

Dumbin mazauna wani gidan yari da ke birnin Benin a jihar Edo sun samu damar tserewa bayan wasu batagari da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun balle gidan yarin.

Duk da babu cikakken rahoto daga kafafen yada labarai, sannan babu sanarwa daga hukumar kula da gidajen yari ta kasa, faifan bidiyon yadda batagarin su ka kai hari gidan yari ya shiga yanar gizo.

A makon jiya ne ma su zanga-zanga a Benin su ka yi korafin cewa wasu 'yan daba sun kai mu su hari yayin tattakin da su ke yi.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ja kunnen masu zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS.

Ministan labarai, Lai Mohammed, ne ya fadi hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba.

DUBA WANNAN: Ba don masu zanga-zanga bane; DHQ ta yi karin haske a kan sabon atisayen 'murmushin kada'

Mohammed ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci tada zaune tsaye ba a kasar nan.

Bayan zanga-zangar lumana wadda matasa suka yi a kan SARS, gwamnatin tarayya ta ja kunnen jama'a, inda ta ce sam ba za ta yarda da tayar da tarzoma ba.

Da duminsa: Bidiyon yadda batagari su ka balle gidan yari suka saki ma su laifi a Benin
Wasu ma su zanga-zanga
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamnatin tarayya ta nuna fushinta akan zanga-zangar.

A ranar Asabar da daddare ne aka nuno Mohammed a tashar talabijin ta NTA yayin da ake nuna shirye-shiryen karshen mako, wato "Weekend File".

Ministan ya yi Alla-wadai a kan yunkurin kashe gwamnan Osun, Adegboyego lokacin da yake yi wa masu zanga-zanga bayani, inda wasu 'yan ta'adda suka kai masa hari.

KARANTA: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga

Ya ce duk wanda ya san farkon fitina bai san karshenta ba. Ya ce dimokaradiyya ta amince da zanga-zangar lumana, shiyasa kwana 11 da suka wuce gwamnati ta zubawa masu zanga-zangar ido.

Amma, yanzu haka, zanga-zangar ta sauya salo, inda 'yan ta'adda suka samu damar cin karensu babu babbaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng