Wacce ta tsira a hatsarin jirgi: Hotunan zazzafar shigar da Kechi Okwuchi ta yi

Wacce ta tsira a hatsarin jirgi: Hotunan zazzafar shigar da Kechi Okwuchi ta yi

- Kechi Okwuchi, wata yar Najeriya da ta rayu bayan hatsarin jirgin sama, na ci gaba da ba mutane sha’awa kan yadda take tafiyar da rayuwarta cikin annashiwa da walwala

- Matashiyar matar ta sanya mutane fadin albarkacin bakinsu a shafin soshiyal midiya kwanan nan bayan ta wallafa wasu hotunanta biyu sanye da wani hadadden kaya

- Mabiya kafar sadarwa ta Twitter sun cika shafinta da sharhi inda suka dunga yaba adonta tare da nuna ra’ayin yin irin dinkin kayan nata

Wata mata da ta tsira da ranta bayan hatsarin jirgin sama, Kechi Okwuchi na ci gaba da birge yan Najeriya da mutane a fadin duniya.

A ranar Talata, 8 ga watan Satumba, matashiyar matar ta je shafinta na Twitter, inda ta wallafa wasu kyawawan hotunanta sanye da wasu hadaddun dinkin kaya na riga da siket wanda ya sa mabiyanta fadin albarkacin bakinsu.

Kechi ta tambayi mabiyan nata ko hotunan nata sun birge su, inda da dama daga cikinsu suka cike sashin da aka tanada don sharhi domin nuna sha’awarsu ga dinkin kayan nata da kuma yadda kayan ya amshe ta.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya

Wacce ta tsira a hatsari jirgi: Hotunan zazzafar shigar da Kechi Okwuchi ta yi
Wacce ta tsira a hatsari jirgi: Hotunan zazzafar shigar da Kechi Okwuchi ta yi Hoto: @Kechi
Asali: Twitter

Wasu daga cikin masu sharhi kan hotunan sun bayyana cewa ta dauke masu wahalar neman dinki.

Da take daukar hotunan cikin salo, da alama Kechi ta bar mabiyanta cikin zullumin wanene telan da ya yi mata dinki.

A lura cewa duk da hatsarin jirgin da ta yi da kuma konewar da ta yi, Kechi na gudanar da harkokinta cike da kwarin gwiwa, lamarin da ya sa take ba mabiyanta sha’awa.

KU KARANTA KUMA: Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa

A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a ranar Asabar, ya dauki nauyin auren marayu su 100 a kananan hukumomin Karasuwa da Nguru da ke Yobe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel