Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

- Dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya zargi mai shari'a, Ayo Salami da laifin shafa masa kashin kaji

- Magu na zargin Mai shari'ar da laifin yada labaran da suka shafesa da kuma yada su ba tare da saninsa ba

- Sakamakon yada labaran, Magu ya fuskanci tsokaci mara dadi da kuma caccaka daga mutane daban-daban

Dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu yana zargin mai shari'a Ayo Salami, akan yada labarai akansa ba tare da saninsa ba.

Dama dakataccen shugaban EFCC na fuskantar kwamitin bincike bisa zargin da ake yi masa na amfani da ofishinsa ta hanyar da bai dace ba, da watanda da dukiyar gwamnatin tarayya daga watan Mayu 2015 zuwa 2020.

Antoni janar, Abubakar Malami, ya mika takardar zargin Magu zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lauyan Magu, Wahab Shittu, a wata takarda da ya ba manema labarai a ranar Lahadi, ya zargi kwamitin da yunkurin kakaba wa dakataccen shugaban EFCC laifi kafin gabatar da korafi a kansa ga shugaban kasa.

Shittu yayi korafi akan yadda kwamitin ta bayyanar da duk wasu kadarori da EFCC suka gano, ba tare da sanin Magu ba.

Kamar yadda takardar ta zo, jaridar Vanguard ta wallafa: "An jawo hankalinmu akan wasu kirkirrarun labarai da aka dauki nauyinsu a wata jarida, wadda aka bata sunan wanda muke karewa, Ibrahim Magu, dakataccen shugaban EFCC, ta yadda Mai shari'a Isa Salami ya shafa masa bakin fenti."

Inda mai shari'ar ya bayyanar da kadarori ba tare da sanin Magu ba.

Sakamakon wannan labarin da suka yada, mutane da dama sun yi ta tsokaci mara dadi ana caccakarsa, kuma hakan yayi karantsaye da dokar 2004, wadda ta hana yada labarai ba tare da tuntubar wanda labarin ya shafa ba.

KU KARANTA: Daliban Najeriya sun bayyana ranar da za su yi zanga-zanga a NASS

Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu
Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu. Hoto daag @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta ja kunnen masu zanga-zangar dakatar da SARS. Ministan labarai, Lai Mohammed ya fadi hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba.

Mohammed ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci tada zaune tsaye ba a kasar nan.

Bayan zanga-zangar lumana wadda matasa suka yi akan SARS, gwamnatin tarayya ta ja kunnen jama'a, inda tace sam ba za ta yarda da tayar da tarzoma ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamnatin tarayya ta nuna fushinta akan zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel