Zanga-zangar #SecureNorth: Ali Nuhu ya yi amai ya lashe

Zanga-zangar #SecureNorth: Ali Nuhu ya yi amai ya lashe

- Jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya lashe amansa kan zanga-zangar tsaron arewa

- A yanzu dai Ali Nuhu ya shiga sahun masu zanga-zangar inda ya wallafa jawabi kan haka a shafinsa na Twitter

- Da farko dai Ali ya ki shiga zanga-zangar bisa wani dalili nasa a kansa

Shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu, ya lashe amansa inda a yanzu ya shiga sahun masu zanga-zangar neman a tsare arewa wato #SecureNorth.

Da farko dai Ali ya ki shiga cikin zanga-zangar bisa wasu dalilai nasa na kansa.

A baya dai, Ali ya sha caccaka a shafin Twitter saboda kin shiga zanga-zangar da aka shirya kan rashin tsaron da arewacin kasar, inda shi kuma jarumin ya bayyana cewa ko kadan hakan bai dame shi ba, kamar yadda sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Zanga-zangar #SecureNorth: Ali Nuhu ya yi amai ya lashe
Zanga-zangar #SecureNorth: Ali Nuhu ya yi amai ya lashe Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Depositphotos

Amma dai ga dukkan alamu a yanzu jarumin ya bi sahun masu zanga-zangar inda ya wallafa wani sako a shafinsa na Instagram na goyon bayansu.

KU KARANTA KUMA: Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa

Ya wallafa a shafin nasa: “Matsalar Tsaro da addabi arewacin kasar nan, ya kamata Hukumomi, Manyan Kasa da kowane dan arewa ya karkato hankalin shi don a kawar da wadannan matsalolin.

"Gaba dayan mu muna da reward da zamu taka wajen ganin an kawo karshen wannan matsalar. #achechijamaa #Securethenorth #EndInsecurityNow #Endnorthbanditry."

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya

A baya mun ji cewa shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya sha suka a wajen yan Najeriya da ke amfani da shafin Twitter.

Hakan ya biyo bayan dalilin da jarumin ya bayar na kin shiga cikin zanga-zangar rashin tsaro a yankin arewacin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel