IGP ya lissafa siffofin sabbin jami'an SWAT da za a fara bawa horo ranar 19 ga wata

IGP ya lissafa siffofin sabbin jami'an SWAT da za a fara bawa horo ranar 19 ga wata

- A ranar Talatar makon jiya ne aka sanar da samar da sabon sashen kwararrun jami'ai wajen sarrafa makamai da yaki (SWAT) kuma za a fara yi masu horo mako mai zuwa

- Matasa ma su zanga-zanga sun nuna rashin amincewa da kafa sashen SWAT domin maye gurbin SARS

- Rundunar 'yan sanda, bayan sauraron korafin matsan, ta zayyana aiyuka da siffofin jami'an sabuwar rundunar SWAT

A ranar Lahadi ne babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya bayyana siffofin sabbin jami'an rundunar SWAT da ka kafa domin maye gurbin rundunar SARS da aka rushe.

IGP Adamu ya bayyana cewa za a fara bawa sabbin jami'an SWAT horo daga ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020.

A cewar IGP Adamu, babu wani tsohon jami'in SARS da aka saka a sabuwar rundunar SARS.

DUBA WANNAN: Yadda Na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo

Kazalika, ya bayyana cewa; "jami'an daka zaba domin bawa horo matasa ne, zakakurai da ke da karfi a jika, sannan kuma sun shafe a kalla shekaru bakwai (7) suna aiki da rundunar 'yan sanda.

IGP ya lissafa siffofin sabbin jami'an SWAT da za a fara bawa horo ranar 19 ga wata
IGP Mohammed Adamu
Asali: Twitter

"Jami'an da aka zaba ma su tsarki ne - ba a taba samunsu da laifi ba a baya, sannan kuma su na lafiyar jiki da koshin lafiyar hankali domin jure duk wahalhalun da ke tattare da horon da za a basu.

DUBA WANNAN: Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Kudu

"Za a yi wa dukkan jami'an sabuwar rundunar SWAT binciken koshin lafiyar jiki, gwajin tu'ammali da kayen maye da miyagun kwayoyi da sauransu.

"Sai wanda ya haye dukkan wadannan gwaji ne zai samu shiga cikin jerin jami'an da za a bawa horo a sabwar rundunar SWAT," a cewar IGP Adamu.

A cikin makon jiya ne rundunar 'yan sanda ta fitar da muhimman abubuwa 9 dangane da sabon sashen rundunar SWAT.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng