Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu

Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu

- Sanata Orji kalu ya ce Awolowo ya sanar da shi cewa bai taba yadda da Babangida ba

- Babangida shine shugaban kasar Najeriya tsakanin 1985 zuwa 1993 a zamanin mulkin soja

- Kalu ya ce Awolowo ya yi watsi da gayyatar da wata kungiyar siyasa ta mika masa karkashin Babangida

Bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce tsohon shugaban yankin yamma, Obafemi Awolowo, ya sanar da shi cewa ya ki aiki tare da shugaban kasan mulkin soji, Ibrahim Babangida saboda bai taba yadda da gwamnatin ba.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewabtsohon gwamnan jihar Abia ya yi watsi da bukatar da aka mika masa na gangamin barin Ibrahim Babangida a matsayin shugaban kasa a wancan lokacin.

Legit.ng ta gano cewa, Kalu a sabon littafinsa mai suna "Rayuwata" ya bayyana yadda manyan jami'an gwamnati suka dinga tuntubarsa domin yakin tabbatar da mulkin Babangida amma ya yi watsi da hakan.

Kalu ya ce Awolowo ya yi watsi da gayyatar da kungiyar siyasar da Babangida ya kafa bayan sun bukacesa da a shiga cikinsu.

Sanata Kalu ya ce: "Awolowo ya sanar da ni cewa bai yadda da sojoji ba kuma ya san basu da niyyar dawo da mulkin farar hula."

KU KARANTA: Hotunan gine-gine 10 mafi darajar kudi a fadin duniya, Ka'aba ne na 1

Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu
Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu. Hoto daga @OrjiKalu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tinubu ya yi magana a kan zarginsa da ake da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS

A wani labari na daban, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Alhamis ya bayyana ranar zaben shugaban kasa mai zuwa.

Ya bayyana cewa, za a yi zaben a ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 idan akwai rai, lafiya da zaman lafiya kamar yadda the Nation ta wallafa.

A sakon fatan alherinsa a yayin rantsar da kwamitin wucin-gadi na musamman a kan sake duba kundin tsarin mulkun kasar nan, shugaban hukumar zaben ya sanar da 'yan majalisar wakilai cewa akwai kwanaki 855 da suka rage kafin zaben.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel