PDP ta lallasa APC, ta yi nasarar lashe zabukan kananan hukumomi a Bauchi

PDP ta lallasa APC, ta yi nasarar lashe zabukan kananan hukumomi a Bauchi

- Ga dukkan alamu, Jam'iyyar PDP na da farinjini mai yawa a jihar Bauchi, duk da Gwamnan jihar dan jam'iyyar ne

- PDP ta lashe dukkan kujerun kananun hukumomi 20, da na kansiloli 323 na gundumomin jihar

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Dahiru Tata ya sanar da hakan a ranar Asabar

Jam'iyya mai mulki a jihar Bauchi, PDP, ta lashe zaben kansiloli da na ciyamomin da aka yi a jihar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi, Dahiru Tata, ya sanar da hakan lokacin da yake gabatar da shaidar nasarar zabe ga ciyamomin.

"An samu nasara mai yawa a zaben kananan hukumomi 20 da gundumomi 323 dake jihar kuma anyi shi hankali kwance.

"Turawan zaben ne suka kawomin sakamakon, ni bayar da shaidar nasarar zabe kawai nazo yi." a cewarsa.

Sababbin ciyamomin da aka zabe sune, Yusuf Garba, Mohammed Baba-Ma'aji, Illiya Habila, Waziri Ayuba da kuma Mahmood na kananan hukumomin Akaleri, Bauchi, Bogoro, Dambam da Darazo.

Sun hada da Muhammed Suleiman, Babayo kasuwa, Dayyabu Kariya, Mohammed Saleh da Abdullahi Maigari na kananan hukumomin Dass, Gamawa, Ganjuwa, Gaide da Itas Gadau.

Duk da dai akwai kananun hukumomi 4 da suka kai kara kotu, wanda yanzu haka ba'a kai ga yin hukunci akai ba.

KU KARANTA: A shirye muke wurin bai wa damokaradiyyar kasar nan kariya - Rundunar soji

PDP ta kawo dukkan kujerun zaben kananan hukumomi da aka yi a Bauchi
PDP ta kawo dukkan kujerun zaben kananan hukumomi da aka yi a Bauchi. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Cikar Ahmed Musa shekaru 28: Tarihi, albashi, dukiya da aurensa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sa hannu akan dokar jihar, wadda ta mayar da Sarkin Kano ya zama shugaba na dindindin ga majalisar sarakunan jihar.

Kafin a gyara dokar ta amince da karba-karbar shugabancin a tsakanin 'yan majalisar 5 na jihar a lokacin da tubabben Sarki Muhammadu Sanusi II yana sarautar Kano.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, a wata takarda yace, "Bayan sa hannu a wannan dokar, Aminu Ado Bayero ya zama shugaban majalisar sarakuna, sannan Gidan Shettima ya zama ofishin majalisar, wanda ba shi da nisa daga fadar sarkin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel