ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

- Fatima Ganduje-Ajimobi, 'yar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ta tofa albarkacin bakinta kan zanga-zangar da matasa ke yi a Najeriya game da 'yan sanda

- Matasan sun kwashe kwanaki sun fita zanga-zanga kan tituna suna neman soke rundunar 'yan sanda ta musamman na SARS da wasu bukatu

- Fatima Ganduje ta shawarci matasa su tanadi katin zabe, su kada kuri'unsu kuma su tabbatar an kirga kuri'un don kawo irin sauyin da suke so a kasar

ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje
Fatima Ganduje-Ajimobi: Hoto daga @fateeaaajimobi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda

A wani rubutu data wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga mutane su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan ya kaɗa kuri'arsa ya tabbatar an kirga kuri'ar tasa.

KU KARANTA: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

"Kuyi zabe kuma kada ku bar mazabar har sai an ƙirga kuri'arku. Kuyi gangami ku raka kuri'unku," Fatima ta rubuta.

"Ku tsaya kai da fata a wajen tattara sakamako sannan ku tabbatar an ƙirga kuri'arku. Matasa sune mafiya rinjaye kuma su za su ceto kasar mu Najeriya. (#ENDSARS #ENDOPRESSION #FGA)," ta sake rubutawa.

Anasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben 2023.

ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje
ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje. @fateeaaajimobi
Asali: Instagram

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta tsare wani ma'aikacin gidan gyaran hali mai suna Danladi Bako bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin tabar wiwi ce.

Mallakar tabar wiwi laifi ne da aka tanadarwa hukunci a sashe na 19 na dokar hukumar NDLEA

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel