Da duminsa: Gwamna Zulum ya alanta Litinin matsayin ranar azumi da addu'a

Da duminsa: Gwamna Zulum ya alanta Litinin matsayin ranar azumi da addu'a

- Gwamnan Zulum ya zabi Litinin matsayin ranar addu'a da azumi bayan ganawarsa da malaman addinin Islama da Kirista

- Ya bukaci mutan jihar su yi addu'a kan masu daukan nauyin yan Boko Haram

- Ya yi bayanin dalilin da yasa yake zuwa wuraren da ke hadari

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Asabar ya gana da malaman addinin Isalam da Kirista inda ya zabi Litinin matsayin ranar addu'a da azumi na biyu a fadin jihar.

Za'a yi addu'an ne domin neman zaman lafiya a jihar.

Zulum a jawabin da yayi, yace ba don alfahari ko neman suna yake zuwa wurare masu hadari ba, amma kawai yana yi domin cika alkawarin da ya yiwa al'ummarsa.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Borno, bayan tattaunawar da mukayi yau, na alanta ranar Litinin, 19 ga Oktoba 2020 matsayin rana ta biyu da azumi a fadin jihar da addu'a na neman zaman lafiya a Borno."

"Ina son bayyana cewa babu hutu ranar Litinin kuma babu wani taron addu'a. Kawai abinda ake bukata shine kyakkyawan niyya da komawa ga Allah yayinda muka azumi daga gidajenmu, ofishohinmu, kasuwanninmu, da wuraren ayyukanmu."

KU DUBA: A ceci jama'a: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci mijinta da hafsoshin tsaro

Da duminsa: Gwamna Zulum ya alanta ranar matsayin ranar azumi da addu'a
Da duminsa: Gwamna Zulum ya alanta ranar matsayin ranar azumi da addu'a Credit: Facebook/Govborno
Asali: Twitter

DUBA NAN: Dalibi ya fille kan malaminsa saboda ya yi batanci ga manzon Allah a Faransa

A wani labarin daban, Rundunar soji ta ce za ta fara sabon atisayen murmushin kada a fadin Nigeria.

Atisayen kamar yadda ya ke a al'adance, ana gudanar da shi ne a karshen watanni uku na kowacce shekara.

A ranar Asabar ne, 17 ga watan Oktoba, Sagir Musa, mukaddashin shugaban hulda da jama'a na rundunar, ya ce za a fara atisayen a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel