Da duminsa: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria

Da duminsa: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria

- Rundunar soji ta za ta fara atisayen murmushin kada na shekarar 2020

- Atisayen wannan shekarar ya sha bamban da na sauran shekarun baya saboda zai waiwayi laifukan da ake aikata wa ta yanar gizo

- A cewar rundunar sojin, atisayen zai fara ne daga watan Oktoba zuwa watan Disamba 2020

SHIGA KA DUBA WANNAN: Ci kyautar N115,000, N75000 ko N38000 ta hanyar shiga gasar rubuta labaru da Legit.ng ta shirya

Rundunar soji ta ce za ta fara sabon atisayen murmushin kada a fadin Nigeria.

Atisayen kamar yadda ya ke a al'adance, ana gudanar da shi ne a karshen watanni uku na kowacce shekara.

A ranar Asabar ne, 17 ga watan Oktoba, Sagir Musa, mukaddashin shugaban hulda da jama'a na rundunar, ya ce za a fara atisayen a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.

Haka zalika, za a kammala atisayen a ranar Alhamis, 31 ga watan Disambar, kamar yadda Mr Musa ya sanar a sanarwar da ya fitar.

Legit.ng Hausa ta gano cewa atisayen na 2020 zai sha bamban da na sauran shekarun baya saboda zai waiwayi ta'addanci ta yanar gizo.

KARANTA WANNAN: An aika takardar korafi a kan Buhari zuwa UK da USA saboda nadin wani mukami

Da duminsa: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria
Da duminsa: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria - Nigerian Army
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, wannan atisayen zai mayar da hankali wajen bincike, ganowa da kuma dakile farfaganda a kafofin sada zumunta na zamani da ma yanar gizo ba ki daya.

Rundunar sojin ta ce wannan shi ne karon farko a Afrika, da aka fara atisaye kan ta'addanci a yanar gizo, kuma a tarihin rundunar sojin Afrika.

Ta kara bayyana cewa atisayen zai taimaka wajen gano 'yan ta'addan Boko Haram da ke guduwa daga shiyyar Arewa maso Gabas da ma sauran sassa na kasar sakamakon matsin lambar daga atisayen sojojin.

KARANTA WANNAN: Gwamantin Buhari ta bayyana sabbin hanyoyin da za ta samu kudaden shiga

Rundunar sojin a ciki sanarwar ta jaddada yunkurinta na tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro a Nigeria ba ki daya.

Ta bukaci daukacin ak'umma da su ci gaba da ba rundunar sojin gudunmowa da goyon baya, har zuwa bayan karewar atisayen.

A wani labarin, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa, Dr. Zainab Ahmed, a ranar Laraba, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da gano hanyoyin samawa kasar kudaden shiga.

Da ta ke jawabi a taron tattalin arzikin Nigeria karo na 26, Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar da ke addabar gwamnati a yau shine rashin kudaden shiga don gudanar da manyan ayyuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel