Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

- Wani dalibi matashi mai shekaru 30 da haihuwa ya auri mata biyu cikin wata guda a kasar Indonesia

- Rahotanni sun ce dukkansu matan biyu da ya aura ba su wuce 'yan shekaru (16) goma sha shida ba

- Mahaifin yaron ya ce ya yi mamakin jin dansa zai auri mata biyu duk da cewa yana makaranta amma ya yi alkawarin tallafa musu

Wani dalibi mai shekaru 20 ya auri mata biyu cikin wata guda a West Lombok da ke yankin West Nusa Tenggara a kasar Indonesia.

An rawaito cewa anyi bikin nasu ne cikin shagulgulan gargajiya da da akafi sani da "nikah siri". Dukkanin amaren basu wuce shekara sha shida (16) ba.

Hotunan auren R da M sun dunga yawo a dandalin sada zumunta ta Facebook wanda hakan ya zama maudu'in da ake tattaunawa a tsakanin masu amfani da yanar gizo.

Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)
Matashi da matansa biyu. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

Da yake bayyanawa wata kafar yada labarai, Kumparan, mahaifi a wajen angon, ya bayyana cewa ya yi mamakin gano cewa ɗan nasa nada sha'awar aure, musamman ganin cewa har yanzu dalibi ne a makarantar gaba da sakandire ta koyon sana'o'i.

DUBA WANNAN: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

"Eh, nayi mamaki. Saboda har yanzu bai kammala makaranta ba. Kuma gab ake da rubuta jarrabawar kasa," mahaifin nasa ya bayyana.

R da M sun kai kimanin shekaru uku suna soyayya, amma R da F sunyi soyayya ne ta ɗan ƙaramin lokaci. Bayan da R ya auri F, sai M da iyalinta suka kai ziyara zuwa gidansu R don tattaunawa da iyayensa, inda anan suka nemi R da ya auri ƴarsu M.

Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)
Matashi da matansa biyu. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

Duk da R, F, da M basu yi magana da wata kafa ba dan gane da auren nasu, iyayen R sun nuna a shirye suke da suyi magana da manema labarai.

Ayuni, yayi korafin cewa zai kashe kudin da yakai miliyan 50, sai dai ya bayyana cewa yana da kyakkwawan zaton ɗan nasa zai ci gaba da karatunsa.

KU KARANTA: FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)
Matashi da matansa biyu. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

"Ina so ɗana ya ci gaba da makarantarsa. Ina da halin da zanci gaba da daukar nauyin karatunsa. Zan iya dauke masa bukatunsa na rayuwa. Kuma zan iya daukar nauyin matansa guda biyu," Ayuni ya bayyana.

Nurminah, mahaifiyar R tana fatan abin da mahaifin nasa yake da, tana fatan cewa auren mata biyu bazai kawo tsaiko ga kammaluwar karatunsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel