Watakila Cristiano Ronaldo ya keta ka’idar COVID-19 – Ministan wasannin Italiya
- Gwamnatin Italiya ta yi magana game da lamarin Cristiano Ronaldo
- ‘Dan wasan gaban Juventus mai shekaru 35 ya kamu da Coronavirus
- Ministan kasar ya na zargin ‘dan wasan bai bi ka’idar takaita cutar ba
AFP ta ce akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya saba dokar yaki da annobar COVID-19 da dawowansa Italiya da ya yi bayan ya kamu.
Ministan wasanni na Italiya, Mista Vincenzo Spadafora, ya yi magana a ranar Alhamis game da dawowar Ronaldo daga kasar Portugal.
Game da saba doka, da aka tambayi Ministan, sai ya ce: “Eh, ina tunanin haka, idan babu tabbatacciyar izini daga hukumomin lafiya.”
KU KARANTA: Ronaldo ya na cikin 'yan wasan da su ka fi kudi a Duniya
‘Dan wasan mai shekaru 35 ya kinkimo jirgin sama ya shigo Arewacin Italiya bayan an tabbattar da cewa ya na dauke da kwayar COVID-19.
Ana zargin ‘dan wasan da saba doka ganin yadda wasu ma’aikatan kungiyar kwallon kasan Juventus su ka kamu da Coronavirus a makon nan.
Amma kungiyar Juventus ta ce: “Cristiano Ronaldo ya dawo Italiya ne a jirgi bayan hukumomin lafiya sun tabbatar ‘dan wasan zai killace kansa.”
KU KARANTA: 'Dan wasa Ronaldo ya saye gidan da kowa zai yi kauyanci a ciki
Ministan wasanni, Spadafora ya ce har yanzu dokar gwamnati ta na aiki, kuma har ga ‘yan kwallo.
Yanzu haka duka ‘yan wasan Juventus su na killace, a dalilin kamuwa da cutar da Ronaldo da kuma ‘dan wasa Weston McKennie su ka yi.
A farkon makon nan ne aka yi gwaji inda aka tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar Coronavirus lokacin da ya ke wasa a gida.
Hukumar kwallon kafa na kasar Portugal ta sanar da haka a wani fitar da jawabi da ta fitar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng